Haƙuri da juriya sai Mata





🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Abbagano✍

Mace Allah yayi mata tsari na wata irin rayuwa, wacce bakowa ke iya irin wannan rayuwar ba.

Farko tana rayuwa a ƙarƙashin iyayen ta, rayuwa mai mutuƙar daɗi da ɗebe kewar ƙanne.

Bayan tayi sabo dasu, sabo mai mutuƙar daɗi, kawai sai wani ya ɓullo yarabata dasu, ya maida ita rayuwa tare dashi!!!

Haka zata fara rayuwa tare da mijin ta tana jin daɗin rayuwa dashi ta hanyar ɗebe mata kewa dayake da kuma kulawa da ita lokaci na farkon aure!!!

Amman ɗan lokaci ƙarami sai miji yafara ƙin zama gareta, yafara Dena bata kulawar data saba samu daga gareshi duk da ta saba dasu!!!

Sannan tazo ta saba da ƴaƴan ta, su zama sune waɗan da suke ɗebe mata kewa a koda yaushe!!!

Suma dai ba jimawa zata rabu dasu' bayan tayi sabo dasu, idan akwai mace cikin ƴaƴan ta, haka zata rabu da ita, domin ta tafi gidan mijin ta itama!!! Idan kuma namiji gareta, haka hima zai yi aure yakoma bawa matar sa kulawa!!!

Tabbas sabo wani abune wanda yake da daɗi a farkon sa' Amman lokacin rabuwa kuwa, ciwo gareshi mai zafin gaske!!!

Amman haka mace zatai ta daure wannan ciwon kashi kashi!!!

Wani abun takaici ma da wasu mazaje Hausawa suke akan matan su, in kaji koka gani sai kai kuka!!!

Kafita kasuwa tun safe' baka dawo ba sai dare, kabar ta gida ita kaɗai babu abokin hira! Amman da ya dawo babu ruwan sa sai yajawo hinfiɗa ya kwanta!!!

Gafarta meyasa bazaka bata lokacin kaba!! Ta hanyar zama ku tattauna!!!

A halittar ɗan adam yana da wani abu da ake kira(حب العطلا) ma'ana son jin labari,

Zaka gane hakan ne lokacin daka ƙaura cewa jama'a na wani lokaci!!!

Duk da hakan mace zatai haƙuri ta zauna gidan mijin ta tana mai hakuri dashi!!!

Girma da daraja a gurin Allah yana ga wanda yaji tsoron sa!!! To nasan mata suna hakuri ne don haka Allah yatsara musu!!!

Allah yakare mana ku matan mu

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post