@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Furta kyakkyawuyar kalma cikin ladabi ga miji na daga cikin haqqoqin da ya hau kan mace saliha.
Dole ne ta kiyaye yin magana ta bacin rai ga mijinta a gaban yara ko kuma dai a gaban jama'ah, ko da kuwa shi din yayi mata abinda bai dace ba. Yin haka koyar da yara mummuniyar tarbiyya ce, kuma cin mutunci ne ga miji.
Na'am, ko da ba a gaban yara bane bai kamata ta qalubalance shi da kakkausar murya ba, domin hakan rashin ladabi ne, amma dai ya fi sauqi da mutunci fiye da yi masa a gaban yara.
KARANTA WANNAN:
◉Masoya Buhari, tamkar masoyan Fir'auna ne a zamaninsa
◉Shelar Bara'a da wulaya, daga Sheikh Ibraheem Zakzaky ranar 5|4|1980 a Funtua
– Funtua Declaration
Idan sabani ya shiga tsakaninsu, to, haquri ake yi har sai sun kebanta sannan tayi masa magana cikin ladabi, domin hakan zai fi sauqi yayi saurin fahintarta.
Ki yi tunani da kyau yaa ke mace saliha, na san ba za ki so ace mijinki yayi miki fada a gaba yara ba, duk da cewa a qarqashinsa kike.
To, idan za ki ji zafin haka, ina kuma ga yin haka gare shi alhali shine sama da ke a shekaru da kuma girman haqqi?
ALLAH YA BA KU IKON KIYAYE WADANNAN HAQQOQI.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~3rd April, 2020.