Gargaɗi Ga Qungiyar Fina-Finan Hausa: Baza Mu Yarda Da Cin Zarafin Jagoranmu Ba – Cewar Mabiya Malam Zakzaky




Wannan gargaɗi ya fito ne daga Almajiran Malamin Shi'an nan a Nigeriya Sayyid Zakzaky suna masu cewa; Muna Jan Kunne ga kungiyar Kannywood cewa ta ja kunnen Dan wasanta wato Shagirigirbau. Domin baza mu yarda da cin mutumcin da ya fara yi ba a cikin fina-finai ga Yan uwanmu dama Jagoranmu ba.

 Domin Yayi wani Video na Shakiyanci wanda a ciki yake tare da wani Tsohon Banza yana zagin Yan Uwa Kai har da Malam Zakzaky (H) ma. Inda yanzu haka Bidiyon yana na nan ana yada shi a wurare daban-daban.

KARANTA WANNAN: Fadar ɗan uwa da ɗan uwa ba'a shiga tsakan: Ba ko wanne Ɗan Shi'a bane Amintacce!

 Kannywood a ja masa kunne sosai domin akan Jagoranmu bama ragama kowaye baza mu aminta da cin mutumcin Aqidarmu ba. Wasan Kwaikwayo ba hauka bane, yana da tsari da Ka'ida. Shagirigirbau ka kiyaye kanka domin baza mu taba yarda da cin mutumcin masu mutumci ba. Allah yasa wannan sakon ya isa ga Kamfanin Fina-Finai na Kannywood da kuma shi mai aikata wannan abu (Shagirigirbau).

Idan kunne yaji Gangan jiii ya tsira, sai a kiyaye.

 - Ibrahim Almustapha Saminaka
  - 4/April/2020 KUBIYOMU A SHAFINMU NA FACEBOOK KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARAI SAHIHAI
Ma'asuma Nigerian News Updates

KUKARANTA WASU LABARAI ANAN 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post