Gakiya Da Gaskiya Mun raba kayan abinci Tirela 276 – a jihohi Uku da aka kulle –Minista Sadiya






A Nijeriya Minista tace sun raba tirela 276 na kayan abinci a jihohi uku da suka kulle sabila da dagile cutar Covid 19


Ministan tace sun raba wa jihohin Legas, Ogun da Abuja kayan abinci cikin tirela 276

Ministar Harkokin Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Farouq, ta ce an raba kayan abinci cikin tirwla 276 ga jihohin Lagos, Ogun da kuma yankin Babban Birnin Tarayya, FCT.

Sadiya ta bayyana haka a ranar Talata a Abuja, lokacin da ta ke amsa tambayoyi a taron kowace rana domin jin irin ci gaban da gwamnati ta samu wajen yaki da cutar Coronavirus.

Idan ba a manta ba, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana sanarwar ware kayan abinci, metirik tan 70,000 domin rabawa ga marasa galihu da zimmar a rage musu radadin zaman gida.

A na sa jawabin, Shugaban Kwamitin Yaki da Coronavirus, kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce an raba tan 6,800 ga Lagos, Ogun da kuma FCT Abuja.

Ya ce ba da dadewa ba za a raba sauran kayan abincin ga jihohi 13 da cutar Coronavirus ta fi yi wa lahani.

A na ta bangaren, Sadiya ta ce har yanzu hukumar ta ba ta karbi kayan abincin gaba daya ba, saboda yawan sa, kuma ba ta da wurin ajiyar sa idan ma ta karba.

“Dalili kenan daga cikin wanda muka rigaya mu ka karba, mu ka debi cikin tirela 276, mu ka raba a jihohi ukun da Shugaban Kasa ya kafa wa dokar fita.

“Nan ba da dadewa ba kuma za mu kara karbowa domin raba wa sauran jihohi 13 da za a a raba wa sauran.” Cewar Sadiya.

Ta kara da cewa akwai sauran kayan abincin yanzu haka jibge a cikin rumbuna ajiye ba a kai ga kwasowa a raba ba.

“Saboda ko metirik tan 2000 zai ci cikin tirela 80. Shi ya sa mu ka bar shi ajiye cikin rumbunan ajiyar abinci.”

Batun rabon kudin da za a ci gaba kuwa, ta ce an yi amfani da shugabannin al’umma, kungiyoyi da kungiyoyin matasa da shugabannin addinai wajen tantance wadanda za a raba wa.

Ta ce za a bi tsarin BVN ne a raba kudaden ga jama’a a wannan karon. Sannan ta ce ana raba kayan abincin ne ga marasa galihu, daidai yadda zai wadace su tsawon watanni biyu kowanen su.

Ko Al’umman jihohin sun amshi wannan kason?

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post