Falalar daren Goma sha biyar (15) ga watan Sha'aban





Hakika Jibrilu (alaihi ssalaam) ya sauko zuwaga Annabi (sallallahu alaihi wa Alihi wasallam) a daren NISF SHA'ABAN,

yace: Ya Muhammad (sallallahu alaihi wa Aalihi wasallam) kayi kokari a wannan dare domin a cikin shi ana biyan bukatu. Sai Manzon Allah(sallallahu alaihi wa Aalihi wasallam) yayi kokari.

Sai Jibrilu (alaihi ssalaam) ya sake zuwa gare shi a karo na biyu, yace: Ya Muhammad (sallallahu alaihi wa Aalihi wasallam) ka yiwa Al'ummar ka bushara cewa: Hakika Allah Ya gafartawa dukkan wanda baya shirka daga cikin Al'ummar ka. Sannan yace: Daga kanka, sai Manzon Allah(sallallahu alaihi wa Aalihi wasallam) ya daga kansa, sai ga kofofin Aljanna, a wata ruwaya kofofin sama dukkan su a bude.

A kofar farko wani mai shela yana shela yana cewa: farinciki ya tabbata ga wanda yayi ruku'u a wannan dare.
A kofa ta biyu wani Mala'ika yana shela: farinciki ya tabbata ga wanda yayi sujada a wannan dare.
A kofa ta uku wani Mala'ika yana shela cewa: farinciki ya tabbata ga wanda yayi addua a wannan dare.

A kofa ta hudu wani Mala'ika yana shela yana cewa: farinciki ya tabbata ga wanda yayi kuka a wannan dare saboda tsoron Allah.
A kofa ta biyar wani Mala'ika yana shela yana cewa: farinciki ya tabbata ga wanda ya aikata alhairi a wannan dare.
A kofa ta shida wani Mala'ika yana shela yana cewa: shin akwai wani mai roko a bashi abinda ya roka?
A kofa ta bakwai wani Mala'ika yana shela yana cewa: akwai mai neman gafara a gafarta mashi?

Sai nace: ya Jibrilu har zuwa wane lokaci ne wadannan kofofin zasu kasance a bude? Sai Jibrilu yace: har zuwa hudowar alfijir. Sannan kuma yace: kuma hakika Allah Yana da wadanda yake yantawa adadin gashin tumakan Bani Kalb.
##*##


Ya Allah albarkacin wannan wata da wannan dare Ka yaye mana COVID 19.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post