Fahimtar al'amarin Wilaya daga mahangar Shaheed Sayyid Ahmad Zakzaky (H)






Sakon Mu'assasatu Abul-Fadl Abbas (A.S)



Me Mumini Ke Bukata Akan Al’amarin Wilaya

Maula Abulfadl Abbas (AS) daga ruwayoyin da suka Inganta sun tabbatar da kasancewarsa Wanda ya samu tarbiya ta musamman daga Mahaifinsa, fikirarsa an gina ta akan basira, don haka a dukkan abubuwan da ya yi don taimakawa Imam Hussain (AS) a Gwagwarmayarsa har zuwa Shahadarsa a filin Karbala yayi su a bisa basira da yarda akan cewa abunda Imam yake so yayi shi ne abunda Allah yake so ayi a daidai wannan lokacin, don haka a dukkan sa’ayinsa a tare da Imam, yana bada dukkan abunda yake iya bayarwa ne don cikar da’arsa da biyayyarsa ga Allah (T).

Shaheed Ahmad a irin nasa Kwaikwayon ya fahimci wannan a matsayin babban sirrin kusanci da Allah da samun yardarsa, zamowa cikin masu wilaya da Wasiyyin Annabi ga Mumini a wannan Zamani shi ne mafi Muhimmanci akan komai. Ta yaya zaka zamo cikin masu cikakkiyar wilaya da Imamin wannan zamanin a wannan lokacin? Amsa wannan tambayar cikin basira, Imani da amsar da yin aiki akan wannan fikirar sune matakai uku da zasu kai mutum zuwa ga samun cikakkiyar wilaya.

KARANTA WANNAN: 
☞ ͡Non Communicable Diseases Part (3)
☞ ͡Zakzaky ne aka zalunta, bashi yayi zalunci ba, balle a yafe masa
☞ ͡Covid-19 da Gwamnatin Nijeriya – Nazari

Nassi daga Hadisin Imam Hassan Al’askari (AS) ya bada siffofi guda hudu (4) na Malami wanda idan ya cika su zai shiga cikin wadanda za a yiwa biyayya da juyawa gare shi don karbar hukunce hukuncen Shari’a irin wannan lokaci na Ghaiba.

Sai dai tafsirin Malamai akan Ma’anar wannan siffofi ya janyo mabanbantan ra’ayoyi akan girman biyayyar da za a iya basu, a bisa fassarar da wasu Malaman suka iya bawa Siffofin sun takaita biyayyar da zaa bawa wanda ya cika su a wasu Ma’aunai da basu kai ga waccan Martaba ta wilaya ba. Sai dai fassarar nassin da sukai hade da iyakance Biyayyar a wani Ma’auni ta fitar da wani Yanayi da zai bar Mumini da kasancewa a wani Zamani da bai da cikakkiyar wilaya, wanda Igiyar da zata hada shi da Allah ta kasance a bisa Shamaki, idan wilayar sa ta kasance a haka, wasu Nassosin na bayyanar da rayuwa a irin wannan yanayin cikin mafi hadari tamkar lokacin Jahiliyya.

Amma a wata fassarar Malaman da Shaheed Ahmad ya karkata zuwa gare ta, tace: wanda ya kasance cikin fakihai (Malamai) mai kiyaye Nafs dinsa (Ma’ana wanda zahirinsa takai Martaba ta Isma) mai kariya ga addininsa (Wanda ya himmatu a ayyukansa da Furucinsa wajen kare Martabar addini daga Makiya) mai sabawa son kansa wajen zabi (Ma’ana wanda a dukkan wani Mataki da zai dauka yana fifita Maslahar addini akan tasa komai tsanani) mai biyayya akan al’amarin shugabansa (Ma’ana wanda Sa’ayinsa yayi daidai da ayyukan Imaminsa a daidai wannan zamani, wanda idan Imamin zai fito daga Ghaiba irin aikin da yake yi zai dora. (…….) a bisa wannan fassara ta wadannan siffofi ta fito da wata Ma’ana ta daban ga wannan Nassi. Wadda zata iya dora wanda ya cika su a matsayin wanda za a jingina kai zuwa gare shi don samun cikakkiyar wilaya.

Da wannan fikirar aka samu gamsashshiyar Amsa da zata cike Mas’alar wilaya a wannan yanayi da Muminai suke ciki. Wanda ya cika wannan sharadin a bisa basira da Fahimtar nassosin da sukai bayanai akan Imamin wannan zamanin zai kasance yana tafiya akan hanya mai shiryatawarwa zuwa ga samun tarbiyyar da idan Imamin zai fita daga Ghaiba mutum yana raye zai kasance cikin Mabiyansa wadanda basu da Shakku ko wani tunani acikin wilaya gare shi.

*Kammalawa*

A wannan lokaci na tunawa da Haihuwar Maula Abulfadl Abbas (AS) wanda Shugabanmu Shaheed Ahmad Zakzaky (H) ya dauke shi a matsayin Samfuri na tarbiyya da gina kai akan Sallamawa da Sadaukarwa, akwai bukatar mu amsawa kanmu tambayoyin da wannan Mas’alar ta wilaya ke dauke shi don samun cikakken Imani.

Ga dukkan wanda ya samu cikakkiyar wilaya, zaku hangi girman Azamarsa da Kumajinsa a wajen tallafawa silarsa zuwa ga Allah, saboda fahimtar da ya samu akan wannan al’amari mai girma. Domin wilaya ce kofar dake kusantar da bawa ga Allah (T) har ya zamo kusancinsa da Hujjar Allah ya kai shi ga biyayyar Allah a cikin dukkan abunda yake aikatawa a dukkan motsinsa, hanya mafi sauki na samun Yardar Allah (T) kamar yadda Shaheed Ahmad Zakzaky (H) ya ambata. IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post