Duk da hani da Saudiyya tayi: Hukumar Alhazan Najeriya na ci gaba da karbar kudin Masu Son Zuwa Aikin Hajjin Bana






Hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta ce har yanzu ana ci gaba da karbar kudin aikin Hajjin bana, duk da yake mahukuntan Saudiyya sun ba da shawarar a dakata tukuna.

Sai dai hukumar ta ce kananan shirye-shirye ne take yi, wadanda ba su shafi kulla yarjejeniya da wasu kamfanoni ba.

A hirarsa da Sashen Hausa na BBC, kwamishinan ayyuka a hukumar Abdullahi Hardawa ya fada wa Umar Mikail cewa shirin “na ko-ta-kwana” ne.

A farkon watan Afrilu ne Saudiyya ta nemi kasashen duniya su dakatar da karbar kudaden jama’a domin zuwa aikin Hajjin bana saboda annobar coronavirus.

Ministan aikin Hajji Mohammed Banten ya ce Saudiyya ta damu da lafiyar Mahajjata sannan ya yi kira ga jama’a su “jira kafin su biya kudin”.

Sai dai Abdullahi hardawa ya ce shirin da suke yi bai shafi kulla yarjejeniya da wasu kamfanoni ba da suke yi wa alhazzai hidima a Najeriya da kuma Saudiyya.

KU KARANTA WANNAN 👇
☞ ͡Covid-19 Da Gwamnatin Nijeriya – Nazari
☞ ͡Wake son gafarar Ubangiji da dawwama cikin farin ciki??
☞ ͡Hijabi: Bin Umurnin Allah ya gagara ma wasu, bare na Donald Trump


“Ai dama ba cewa aka yi ba za a yi Hajji ba, saboda haka za mu iya ci gaba da kananan shirye-shirye, duk lokacin da Allah ya sa annobar ta wuce mu ba za mu samu matsala mai yawa ba,” in ji shi.

Ya kara da cewa: “Mahajjata suna bai wa hukumomin jihohi kudinsu sannan a yi musu rajista kuma ba za mu katse musu hanzari ba.”

Kazalika ya ce da yawan mahajjatan ba lokaci guda suke biyan kudin ba, saboda idan lokaci ya kure ba za su iya biya ba.

“Idan Allah ya kaddara ba za a yi Hajji ba to za a mayar wa masu bukata kudinsu,” a cewarsa.

Ya kara cewa da ma ba sabon abu ba ne wasu su bukaci a mayar musu da kudinsu, wasu kuma kan bari sai shekara ta gaba sai su karbi kujerar.

Ana sa ran fiye da Mahajjata miliyan biyu ne za su tafi Makkah da Madina a watan Yuli zuwa Agusta domin gudanar da aikin Hajji.

@Bin Haroun Sigau

 KARANTA MUHIMMAN LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post