Drama: Gwamnatin tarayyar Najeriya tace; har yanzu bata ga ko sisin Kobo, daga Alƙawuran da kamfanoni keyi, na bada tallafi don yaki da Covid-19



Ma'asumah Nigerian News Update

Wan'nan Dirama ko film yayi mun kyau kwarai da Gaske.

Ashe farau bata da daɗi sai ramau?

Wan'nan sai ya tuna mun da labarin wani Ɗan fulani mai shegen wayo.

Anyi wani Ɗan fulani, Attajiri (mai kudi) wata rana yaje kasuwa danufin zai saida Ɗan maraƙin sa.

Bayan anyi ciniki ga mai saye, ya saya ya biya, Dan fulani yana cikin tusa kuɗi don ya tabbatar sun cika, sai ga maroƙi da abin kiɗi ya ƙaraso wajen wan'nan ɗan fulani yana ƙidi yana kirari.

Makaɗi= bayan sautin ganga yacigaba da rafka kirari. Kaine ɗan sarkin fulani! Jikan sarkin fulani!! Fari mai farar aniya!!! Kayi taƙama yanda kake so, uwa da uba kai jinin sarauta nekaima sai kayi sarkin fulani.

Ɗan fulani yaji daɗin wan'nan kirari sosai har ya fara ɗaga kai yana taƙama gami da rausayawa, amma abinka ga mai wayo, sai ya ƙi bashi ko sisin kwabo, sai yace.

Ɗan fulani= Kaje gida gobe ka amshi Nagge nabaka kyauta.

Jin wan'nan kyauta da Dan fulani yayima maroƙi, sai ya sanya ya kurma ihu, don daɗi gami da ƙara buga ganga.

                             WASHEGARI
Maroƙi, ya siyo ƙatuwar igiya mai shegen kwari yatafi gidan Ɗan fulani, yayi masa sallama, ɗan fulani ya fito, bayan sun gaisa.

Ɗan fulani yama nuna baigane maroki ba, saida maroƙi yayi ta masa kwatance sai ɗan fulani yace.
Ɗan fulani= Ayyo nagane ka wan'nan maƙaryacin da muka haɗu kasuwa? Ko ba kai bane?

Nan take fuskar maroƙi ta canja yaji ankirashi maƙaryaci.     Maroƙi yace, Kamar yaya maƙaryaci?

Danfulani yace= Eh mana maƙaryaci, ka iskeni kasuwa ina ƙirga kuɗi kayi mun ƙarya, kace ni ne ɗan sarkin fulani kuma jikan sarkin fulani, lokacin da ƙana sheko ƙaryar nan kam naji daɗi, kuma ka sanyani girman kai.

To nima sai naga tayaya zansaka maka da daɗin da kajiyar dani, sai naga ƙarya kaimun nima bari inrama, sai nace nabaka kyautar Nagge, kuma ƙarya nake. Lokacin da nace nabaka Kyautar Nagge bakiji daɗiba?

Maroƙi yace= lallai kam naji daɗi,
Ɗan fulani yace, Nima da kakirani da Dan sarkin fulani naji daɗi, kaga kaimun ƙarya nima nayi maka ƙarya duka munji daɗi, babu bashi.

Maroƙi dai yaga lallai Ɗanfulani ba bashi Nagge zaiyi ba yace to 'yallabai don Allah ko akuyace kabani, Danfulani yace wallahi ko kabar mun gida ko insamaka sanda.

Gwamnatin Nijeriya tayima talakka arƙawari, zata tallafa mashi da ƙudi domin rage raɗaɗin zaman gida da aka tilastamana talakka yaji daɗi yakuma sanya rai, lokaci ɗaya Gwamnatin da kanta kuma ta ƙaryata cewa ita batace ba.

Don wasu, suma sunyi al'ƙawari sun karya sai abin yazama abin tsogomi.

Inakira da masu ƙudi da kamfanoni don girman Allah kada kuba Gwamnatin nan ko Kwandala, saboda ko kun bata bazataba talakka ba zasu azurta kansu ne suzo suna zagin mu suna cewa bamu da haƙuri.

Idan akwai hanyar da zaku iya taimakon talakka kaitsaye tsakanun ku dasu kutaimaka masu, idan kuma babu to don Allah ku kulle aljihun ku, Gwamnati batada imani.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post