Dokoki 17 da ke kan mace saliha (17)






@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MIJINKI NE MAFI GIRMAN HAQQI A KANKI

Saboda girman haqqin mahaifa akan 'ya'yansu sai Allah (T) ya gwama yin godiya gare shi cikin ni'imominsa da yin godiya gare su (mahaifa)don mu san darajarsu da matsayinsu.

Inda yake cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

" KA GODE MIN DA KUMA MAHAIFANKA ...."

Sai dai kuma duk da wannan matsayi na iyaye sai ya fifita matsayi/ikon miji akan matarsa fiye da haqqin iyaye tare da cewa ba wai ya tauye girman haqqin nasu bane.

Duk lokacin da aka ce mace tayi aure, to, miji shine mafi girman haqqi a kanta wajen zartarwa, hani ko tabbatarwa.

Haqqi ne a kanki ya zamana cewa shine mai maganar qarshe a kanki, da ace umarnin aikata abu mabambanta zai fito daga gare su, wato umarnin miji ya sabawa umarnin mahaifa, to, umarnin miji ake dauka abar na mahaifa matuqar umarnin mijin ba bisa sabawa mahalicci bane.

LATSA NAN👇
Ranar lafiya ta duniya: Qalubale ga gwamnatin Nijeriya
Happy birthday to the golden son of 21st century Sheik Zakzaky
Imam Mahadi (Ajtfs): Wacce tambaya kake tsoro Imam yayi maka???

Maganar 'ya'yanki da ta qawayenki ba sune abin dubawa ba matuqar abinda suka fada ta sabawa ta mijinki, sai dai idan maganar tasu kan umarni da kyakkyawa ne, to, anan sai a bar ta miji matuqar tasa maganar ba akan shiriya take ba.

Amma fa cikin hakan dole ki kare martabar mijin naki ba tare da nuna masa cewa su sun fi shi bane.

Ki riqa nuna masa a kullum cewa shi yafi kowa daraja a kanki ta hanyar zantukanki da ayyukanki, ba wai a bakinki ki nuna hakan ba, amma a aiki kuma ki nuwa shi ba komai bane.

IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

09039791509-08126385470

~9th April, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post