@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KI JANYO MIJINKI KUSA DA KE FIYE DA KOWA
Iya tarairaya, fara'a da dadadan kalaman soyayyah (sweet cutes love)ga miji na daya daga cikin manyan sinadarai na qara cusa soyayyarki cikin lambun zuciyarsa.
Ke ya caccanta ki nuna masa dukkan wata kula ta musamman fiye da wani, kada ki kuskura ki bar wani/wata ta riqa ba shi kuwa da dukkan wasu hanyoyi da za su iya cusa soyayyarsu cikin zuciyarsa.
Abokanki/qawayenki na da matsayi a wajenki wadanda za ki riqa jansu a jika ta hanyar kyautatawa da dai wasu abubuwa, domin Annabi (S.A.W.W)na cewa;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ MAFI ALKHAIRIN ABOKI SHINE WANDA YAFI KYAUTATAWA ABOKINSA .‘’
Saboda haka, za ki iya kyautata musu, amma kada ki yarda ki ba su qofa ta yadda za su sami damar kusantar mijinki (with any means).
Amma kada ki zarge shi don ya kyautata musu kamar yadda kike kyautata musu, yin hakan taimakonki ne da nuna cewa yana sonki.
Idan ba ki manta ba ai Annabi (S.A.W.W)ya riqa kyautatawa qawayen Sayyidah Khadijah har ma bayan wafatinta (S.A), kuma don tsananin soyayyarta gare shi yake kyautatawa qawayen nata.
MIJINKI ABIN ALFAHARINKI!
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509-08126385470
~6th April, 2020.