Dokoki 17 da ke kan mace saliha (14)





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Tsabtar miji abune da ke gara danqon soyayyah tsakanin miji da mata, kuma rashinsa kan haddasa qiyayya da hangen wani ko wata daga waje.

Tsabtarsa anan ba wai ta taqaita ga jikinsa bane, a'a, ya hada da makwancinsa da kuma abincinsa.

Kula da tsabtace abinci da gyaran gurin kwanciyar miji haqqi ne da ke kanki yaa ke saliha. Ba zai taba zama daukakarki ba ki kasance kina barin mijinki da gyaran makwancinsa, ko da kuwa yana da turaka ce wacce ba tare da ke yake kwanciya a gurin ba.

Akwai wasu mata qazamai wadanda ba sa kula da dakin kwanansu ballantana makwancin mijinsu, kuma sukan tara tsummokara masu datti cikin daki yadda miji ne ke qoqarin kawarwa don gudun abin kunya.

Kada ki kasance mai sakaci har ya zama shine zai riqa kula da wannan aiki, domin hakan zai sa ya raina miki tare da hango wata da ke waje a matsayin mai faranta masa fiye da ke.

ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

     09039791509

~5th April, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post