Tsohon Limamin Masallacin Harami dake birnin Makkah, wanda ya shahara sosai a duniya, ya bayyana cewa ya daina yiwa ‘yan shi’a kallon kafirai a yanzu.
Bayan shafe shekaru goma yana Fatwar cewa ‘yan shi’a kafirai ne, Adil ibn Salim Al-Kalbani, tsohon shugaban limaman Masallacin Harami na Makkah, ya bayyana a gidan talabijin cewa daga yanzu tunanin shi ya canja akan ‘yan shi’ar.
KARANTA WANNAN👇
➝Imam Mahadi (Ajtfs) Fita Na Biyar (5)
➝Non Communicable Diseases Part (1)
➝Covid-19 da Gwamnatin Nijeriya – Nazari
A hirar da yayi da gidan talabijin na MBC a kasar Saudiyya ya ce: “Duk wani wanda ya yarda cewa akwai Allah, kuma yake cin naman layya, sannan kuma yake kallon al-qibla yayi sallah, tabbas wannan Musulmi ne.”
“Na rantse da Allah babu wani wanda ya sanya ni na rike wannan ra’ayin nawa a raina,” inji Malamin.
KA SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Labaran Duniya