Mun sami labari daga majiya mai ƙarfi cewa; Bayan faruwar hakan, yan sanda sunyi awon gaba da ilihirin manyan gidan baki daya.
Sudai wadannan mutane mazaunan Lere ne dake jahar Kaduna.
Dalilin da yasa suka kashe wannan matashi kuwa zamu iya kiran sa da tsautsayi, domin matashin yayi kaurin suna wajen sace-sacen kayan lambu.
Darabon dai wannan satar da yayi itace karshen numfashin sa. Domin a wannan karon ya sati Attaruhu (Kayan miya) a lambun wani bawan Allah.
Bayan sun sato ne shida abokin sa mai lambun ya hadu das u harya shaida kayan lambun sa, daga bisani ya amshe kayan sa.
KARANTA WANNAN: Falalar daren goma sha biyar (15) ga watan Sha'aban
◉Dokoki 17 da ke kan mace saliha (15)
◉Tarihin Imam Mahadi (Ajtfs) na (2)
Ashe dai rabon wahala, ya ije Attaruhun ya tafi sallar Magrib, suka bi suka kara saukewa. Shine yakai kara wajen mahaifin sa.
To, abinka da mai haki, shune yan uwan mahaifin da mahaifin kansa suka saka yaron a gaba da duka, har takai ma jini na fita ta baki da kunnen yaron, har allah ya karbi kwanan sa, yace musu ga garin ku nan.
Allah shi kyauta, ya kare mu da aikin danasani.
Daga wakilin mu, Bin Haroun Sigau
Tags:
Labaran Duniya