Daga cikin mafi girma da kyawun abin da Musulunci ya yi kira zuwa gareshi shi ne; ‘Yan’uwantaka tsakanin musulmi a kan duk sassabawarsu, martabobinsu da mukamansu.




Kamar yadda mafi munin abin da musulmi suka yi a yau da kuma kafin yau shi ne, sakacinsu wajan riko da wannan 'yan uwantaka ta Musulunci.

Domin mafi karancin koyarwar wannan
‘yanuwatakar ita ce “Ya so wa dan’uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, kuma ya ki masa abin da yake ki wa kansa, kamar yadda zai zo a hadisin Imam Sadik (A.S).

Ka duba ka yi tunani a kan wannan dabi’a mai sauki a mahangar Ahlul Baiti (A.S), zaka samu cewa yana daga mafi wahalar abin da zaka iya samu wajan musulmi, da musulmi zasu yi wa kansu adalci su san addininsu sani na hakika, su yi riko da wannan dabi’a ta so wa dayansu dan’uwansa abin da yake so wa kansa, da ba a ga zalunci daga wani ba ko ketare iyaka, ko sata, ko karya, ko yi da wani, ko annamimanci, ko zargi da mummuna, ko suka da karya, ko wulakanci, ko girman kai.

LATSA NAN👇
☞ ͡Ku cika azumin ku, zuwa dare" – Faɗar Allah (T)
☞ ͡Iyali A Muslunci... Fita Na Uku (3)
☞ ͡Hukuncin Shan Ruwa


Idan da musulmi sun tsaya sun fahimci mafi karancin ma’anar hakkin
‘yan’uwantaka a tsakaninsu kuma suka yi aiki da ita, da zalunci da ketare iyaka sun kau daga bayan kasa, kuma da ka ga ‘yan Adam sun zama ‘yan’uwa suna masu haduwa da juna cikin farin ciki, kuma da mafi daukakar sa’adar zamantakewa ta cika garesu, kuma da mafarkin malaman falsafa na da na samar da mafificiyar hukuma ya tabbata, da sun kasance masu musayar soyayya a tsakaninsu, da ba su bukaci wasu hukumomi da kotuna ba, ko ‘yan sanda, ko kurkuku da makamantan su

Dafatan allah ya bamu ikon rike Yan'uwan taka

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post