Covid-19: Ƙasar Chadi ta baiwa tsohon shugaban ƙasar ta, da ke tsare a gidan kaso Hutun wata biyu ya dawo gida domin gudun kada ya kamu da cutar CORONAVIRUS.





Tshohon shugaban ƙasa Hebri dake tsare, tsawon shekaru ana tuhumarsa da keta haƙƙin Dan Adam kisan 'yan ƙasa da fyaɗe.

KASAR NIGER:-Ta sallami babban Shugaban' Yan adawar ƙasarta Hamou Amodou dake tsare agidan kaso tsawon lokaci bisa zargin, safarar yara da keta alfarmar ƙasar, shima an yafemasa laifukan nasa ne, saboda gudun kada yakamu da cutar CORONAVIRUS a gidan kaso, inda yake a tsare.

Zaharaddeen Ishaq Abubakar.

KASAR NIGERIA Ta kama malamin Addinin musulinci Sheikh Ibrahim Elzakzaky tsawon shekara hudu/biyar tana tsare, bisa zargin ya tare Babban titin shiga cikin garin Zariya yana gudanar taron Addini.

Bayan dokokin ƙasa sun yarda, ko wane ɗan kasa yayi addinin sa iya fahimtar sa batare da tsangwama ba, kuma abashi kariya.

Duk'da wan'nan damar da Kundin tsarin mulkin Nigeriya ya bada, na kayi Addini iya fahimtar ka, bai hana Shugaba muhammadu Buhari a ƙarƙashin jagorancin rindunar tsaron sojojin sa su afkama 'yan shi'a da malamin su ba.

A inda suka afka masu da muggan makamai irin na yaƙin kasa da kasa, suka kashe ɗaruruwan mabiya shi'a yara da manya harda mata masu ciki da tsofi, Suka kashe 'ya'yan malamin masu ƙananan shekaru, guda uku, suka kashe, yayar malamin mai shekaru saba'in aduniya suka kuma ƙone gawar ta.

Sojojin Nigeriya da Umarnin Shugaba muhammadu Buhari basu tsaya anan ba suka kashe manya manyan nakusa da malamin, bayan da suka kama sama da mutum ɗari bakwai suka ɓatar wanda har yanzu ba'a san inda suke ba.

Bayan haka kuma suka buɗe ma malamin da matarsa wuta, sukaimasa harbin da badon yatashi ba, amma Allah ya hana ya mutu, suka jashi cikin jini shida matar sa suka kai shi gidan kaso, suka tsare, sakamakon harbin da sukai masa ya sakamar masa guba acikin jiki yanzu haka ya rasa idonsa guda, kuma babu ishashshen jini a jikinsa ga stroke, da hawan jini, a tattare dashi.


KARANTA WANNANYawan shekaru ba shine girma ba a harka, sallamawa ce!

Agefe guda kuma gubar harsashi nata ƙara yaɗuwa ajikin sa, ayayin da matar sa kuma take zubar da jini ta hanci, saboda tasirin gubar harsashe yasanya ko tsayuwa bata iyayi da ƙafafun ta.

An hanasu ganin likitocin su ballan tana ayimasu aiki ko taimakon gaggawa.

San'nan Gwamnatin kaduna ta jagoranci rusa duk'wani gini mai alaƙa da malamin, ɓarnar bata tsaya anan ba, hatta ƙabarin mahaifiyar malamin da ƙabarin 'ya'yan sa. da Gwamnatin tshohon shugaban ƙasa janathan ta kashe saida sukabi suka rusa.

Kuma sukayi iƙirarin haka bayan sun tabbatar ma da wani kwamitin jeka nayika da Gwamnatin Nasiru El'rufa'i ta kafa domin ya binciki lamarin. Da bakinsu sukace sun kashe 'yan shi'a ɗari uku da arba'in da bakwai (347) yara da manya mata da maza kuma sunyi ƙaton rami sun zubasu waje ɗaya sun bizne.

Kotun Nigeriya dake zamanta a Abuja ta yanke hukunci cewa an zalinci malamin, dole abiyashi diyya ta miliyan hamsin, dashi da matar sa, akuma gina mashi gida duk'inda yakeso a arewcin Nigeriya kuma abashi kulawa ta musamman, amma Gwamnatin Shugaba buhari tayi kunnen Uwar shegu da hukuncin dokokin ƙasar.

Acikin irin wan'nan lokaci da duniya take fuskantar fushin Ubangiji sakamakon zubda jinai nai na bayin Allah raunana, a ko'ina aduniyar, Allah ya jaraba al'ummu da wata muguwar annoba da lokaci ɗaya ta canja tunanin masana da manyan kwararrun likitoci da falosafas na duniya, yasanya ko wace ƙasa yanzu aduniya tana sallamar miyagun masu laifi da ke tsare a gidajen kaso,domin tausasawa don gudun kada annobar ta shafe su.

Itako Nigeriya a ƙarƙashin jagorancin shugaba buhari cewa tayi tasamar da yanayi mai kyau da zai taimaka ma bursunoni yanda Annobar CORONA bazata shafesu ba.

Bayan rahotanni sun bulla cewa ansamu wasu mutum biyu masu cutar a gidan kaso na Kaduna wanda ya sabbaba bore ga 'yan gidan kason, har sojoji suka kashe mutum biyar daga cikin su, a wani rahoton da Sahara Repoters ta fitar.

A irin ƙasa kamar Nigeriya da cin hanci da rashawa yayi katutu, kuma yashafi duk wani ɓangaren ma'aikatu dake Nigeriya, a irin wan'nan ƙasa take da shuwagabanni marasa adalci da imani da sukafi ƙaunar karen gidansu bisa ga talakka, a irin wan'nan ƙasa da basu maida ran ɗan adam bakin komi ba, ƙasar da bata da likitoci bata da kayan aiki, su kansu shiwagabnnin sun san da haka shiyasa basa zama ƙasar a yayin da wata cuta ta same su sai sun tafi kasashen turai, wai sune suke cewa sun samar da yanayin da cutar CORONA bazata shafi 'yan gidan kaso ba.

Don haka nake so inyi amfani da wan'nan damar in yi kira ga shugaba muhammadu Buhari da lallai inajan hankalin ka da kasaki Malam Zakzaky da matar sa da sauran waɗanda kuka ɓoye, domin sunemi lafiyar su, tunda kotu tace a sake shi, kuma kuntabbatar bashi da laifin komi.

Dafatan Allah ta'ala ya taimakemu ya taimaki ƙasar mu, ya bamu zaman lafiya, Allah ya kauda miyagun azzaluman ƙasar nan, Allah ya taimaki talakkan Nigeria ya bashi mafita.

IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

 Daga wakilin mu,
Zaharaddeen Mziag
07/04/2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post