FALALAR ALLAH DA YAWA TAKE.
*Zaharaddeen mziag* 04/0/2020
Alhamdu lillah!
Munayi masu fatan Nasara Allah ta'tala ya dafa masu ya taimaka masu akan wan'nan abin Alheri da cigaba da suke ƙokarin aiwatarwa.
Wan'nan ƙadai ya isa yasanya muyima Allah abinda yakeso koda kuwa uwar korona bairos zata kashemu.
Allah (T) ya aramamu lafiya tsawon shekaru, ayayin da Gwamnati ta gaza wajen taimaka mana da asibitoci, ya saukar mana da arziƙin ruwan sama duk'shekara muna Noma muci musha min rizƙillah, a yayin da Gwamnati take azabtar damu da rashin ruwan famfo.
Allah (T) ya bamu lafiya da izinin shiga ko ina aduniya domin nema, wato kasuwanci, da bautar sa.
يعبادى الذين ءامنوا ان ارضى وسعة فايى فاعبدون
Amma Gwamnati ta hana.
Da gangan ammaidamu mabarata, ammaidamu jahilai, wan'nan kuma shine galaba a wajen mahukunta, domin kuwa babu yanda za'ayi kasan cewa ana zalintar ka sai idan kanada ilimi, an kassara ilimin an yunwatar damu, kullum bin mahukuntan muke suna watsamana tsaba kamar kaji, ta janibi guda kuma karen gidansu yafimu daraja, Eh mana! Ai abincin da karensu ke ci kai talakka tunda kake baka taɓa ganin irinsa ba, kuma inda za abaka kuɗin sa, na rana ɗaya zakayi sati kana ci basu ƙare ba.
Agefe guda kuma haka ma ba'a kyalemu ba kashemu ake kamar tururuwa, idan ka cire ƙasar yeman da Amerika ke kashe al'uma a ƙarƙashin jagoranci saudiyya, a duk duniya babu ƙasar da akafi kashe mutane kamar Nigeria.
INA MAFITA?
Alal aƙalli kai talakka kanemi ma'abota Allah, su sanar da kai Allah, domin kada kayi taɓi alaikum, (biyu babu) saboda duk wan'da yatashi Nigeriya yarayu irin wan'nan rayuwar ta ɓakin ciki da ƙaskanci talauci da zillah, kuma ya yarda yaje wajen Allah bai samu Aljanna ba haƙiƙa yayi babbar hasara.
Don haka yakamata talakkan Nigeriya ya je wajen malamai na Allah ba na Gwamnati ba, kuma wallahi dukkan su basu da wahalar ganewa, musamman wan'nan lokacin da gaskiya take kamar hasken rana, ga ƙaramin misali, mafiya yawa malaman nan sunada cutar CORONAVIRUS ko ajiki ko azuciya, saboda sun ruga sun cuɗanyu da masu mulkin da suka je ƙasashen turawa suka kwaso mana ita.
Dani da kai da ke da ku da sauran duk wani mai hankali, ƙarara yasani cewa ƙasar nan Azzalumai ke mulkin ta, shikuwa Azzalumi bashi da abokin faɗa sai maƙiyin zalunci, don haka a matsayin ka na mai hankali, sai kayi amfani da shi kagano waɗanne malami ne kai tsaye Azzaluman mahukuntan ƙasar nan suke faɗa dasu?
Idan kagano to wallahi summa tallahi billahillazi la'ilaha illahuwa! Waɗan'nan malaman mafita na hannun su, kai Aljannama a wajensu take, idan kabisu zaka tsira duniya da lahira.
Idan kana shakku, malam talakka kaje kabinciki tarihi kagani wane Annabi ne, mahukuntan zamanin sa basu yaƙeshi ba? Idan kuwa hakane Ashe sunnar Allah bata canjawa.
سنة الله فى الذين خلوا من قبل ولن تجد لسنة الله تبديلا
To waɗan'nan malaman suke tare da Allah Allah yana tare da su, sune zasu fassara maka Al'qur'ani kamar yanda yazo daga wajen Allah ta hannun bawan sa Muhammadu Rasulullah(S.A.W) wajensu zaka san daga inda aka fito, kumu ina za'aje?
Suna zasu fassaramaka haƙiƙanin haƙuri da 'yan wantaka da soyayya ta gaskiya a musulinci
Sune zasu fassara maka rayuwar Annabi ta haƙiƙa ji da gani a aikace ba shaci faɗi ba.
Dafatan Allah ya bamu lafiya da zama lafiya Allah (T) ya kawomana ƙarshen zalinci da azzalumai, Allah ya taimaki musulmi da musulinci, Allah ya haɗa kawunan mu cikin soyayyar juna da ƙauna. Wasallahumma ala rasulillah wa Ahalubaythi.

Tags:
Cuta da Magani