Coronavirus ce kalubale ma fi girma tun bayan yakin duniya na biyu II'

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya yi gargadin cewa annobar coronavirus ce kalubale ma fi girma da duniya ta taba fuskanta tun bayan yakin duniya na biyu.

Mista Guterres ya bayyana haka ne a wurin kaddamar da wani rahoto kan yadda annobar za ta shafi tattalin arzikin duniya, inda ya ce annnobar za ta iya haddasa rikicin tattalin arziki "wanda ba a taba ganin irinsa ba a baya-bayan nan".

Wannan gargadi nasa yana zuwa ne a daidai lokacin da ake hasashe kan yadda matakan da ake dauka na yaki da coronavirus za su shafi tattalin arziki.

"Covid-19 ce ma fi girman kalubale da muka fuskanta tun bayan kafa Majalisar Dinkin Duniya," in ji Guterres.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi hasashen cewa za a rasa aikin yi kusan miliyan 25 a fadin duniya sakamakon annobar. Sannan ya yi hasashen cewa kudaden zuba jari ma za su ragu da kusan kashi 40 cikin 100.

Adadin wadanda cutar ta yi ajalinsu a fadin duniya ya kai kusan 42,000 sannan kusan 860,000 suka kamu.

Fiye da mutum 4,000 ne suka mutu a Amurka sakamakon cutar - sama da na kasar China, inda cutar ta fara bulla a karshen shekarar bara.

Jami'ar Johns Hopkins ta ce mutum 865 sun mutu a cikin awa 24 da suka gabata a Amurka, sannan mutum 189,000 ne suka kamu da cutar a kasar.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post