A wata sanarwa da kungiyar yada labarai  ta fitar, wadda Kakakin Yada Labarai Ben Goong ya sa wa hannu, ya ce iyayen dalibai su yi kaffa-kaffa da labarai na boge da na soki-burutsu.
Yace har yau Gwamnatin Tarayya ba ta aza ranar da dalibai za su koma makaranta ba. Maimakon haka, an shawarci iyaye su bi umarnin gwamnati na daukar dukkan matakan da suka wajaba domin kauce wa kamuwa ko yada cutar Coronavirus a cikin jama’a.
Ya ce sanarwar da aka watsa, wadda a ciki har aka ce Ma’aikatar Harkokin Ilmi ta dora yajin aikin malaman jami’o’i a kan shugabannin jami’o’in, karya ce, kuma takardar sanarwar ta bogi ce karara.

KU KARANTA NAN 👇

 Ɗumi-Ɗumi: Yaron gwamna Nasir El-Rufa'i yayi wa wani ɗan Ƙabilar Igbo Barazanar yiwa Mahaifiyar sa Fyaɗe
☞ ͡Kayi abinda ƴan Nijeriya zasu riƙa tunawa dakai bayan kabar mulki – Sakon Gwamnan Sokoto Ga Shugaba Buhari
☞ ͡Sojojin India da Pakistan sunyi musayar wuta a yankin Kashmir, Mutum biyu sun rasa ran su


Gwamnatin Tarayya ta bayar da hutun zaman dirshan a gida ga dukkan daliban firamare, sakandare, manyan makarantun sakandare da kuma jami’o’in kasar nan, biyo bayan bullar cutar Coronavirus a Najeriya.
Haka nan kuma ance wa ma’aikatan gwamnatin tarayya daga masu mataki na 10 zuwa 12, duk an ce su ci gaba da zaman gida.
Har yanzu ba a gano maganin cutar coronavirus a duniya ba.
Kasar Amurka ce tafi shiga cikin halin ha’ula’i game da wannan cuta.

Daga shafin jaridar Premium Time Hausa.
Tare da wakilanmu;
Auwal Tukur