Sai Dai Inna fada Kuji ba Dadi, Amma Sahabbai Ne Farkon 'Yan Bidi'a..!!!





"Ko wacce Bidi'a bata ce"


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

SAHABBAI NE FARKON 'YAN BID'AH

Kalmar bid'ah a Lugga ita ce dukkam wami fararren abu, amma a shari'ah (ISTILAHAN)shine duk wani aiki wanda Annabi (S.A.W.W)bai aikata shi ba, sannan bai yi umarni da aikata shi .

Sai dai sabanin da aka samu ko kuma nace abinda wasu jahilai suke cewa shine, wai dukkan wata bid'ah bata ce, kuma wai bata wuta ce. Kan haka suka radawa wata qunqiyarsu suna da masu kawar da bid'ah.

Wani abu guda da suka jahilta shine, Annabi (S.A.W.W)na cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ NA HORE KU DA BIN SUNNATA DA KUMA SUNNAR KHALIFOFINA SHIRYAYYU MASU SHIRYARWA, KUYI RIQO DA ITA DA FIQOQINKU (your canises) .‘’

Bisa nazari za mu fahinci sunnar Annabi (S.A.W.W)abune dabam, ta Khalifofinsa ma dabam. Domin da ace dukka iri daya ce, to, da baice sunnarsa da ta Khalifofinsa ba, domin duk wanda ya aikata abinda wani ya fare shi kafin shi, to, wannan abin ba nasa bane na wanda ya rigaye shi.

Yanzu idan muka duba cikin Muwadda ta Imamu Malik, qarqashin babin azumin watan Ramadan za muga ance sallar Tarawihi Umar Bn Khaddab ne ya qirqirota, ba sunnar Annabi (S.A.W.W)bace.

Shima da kansa ya ambace ta da bid'ah ce.

KU KARANTA NAN👇
☞ ͡Ku tambaye ni kafin ku rasa ni Fita Na Ɗaya (1)
☞ ͡Du'a Muqatil| Addu'ar biyan bukata da gaggawa
☞ ͡Wallahi akwai maganin Covid-19 a Najeriya Ku tambayi Zakzaky –Inji Wani Bawan Allah

‘’ NI'IMA BI BID'ATU HAAZIHI .‘’

Sannan cikin Sahihul Bukhari ya kawo cewa, kiran sallar juma'ah a zamanin Annabi (S.A.W.W)da Abubakar da Umar sau daya akeyi, amma a zamanin Usman Bn Affan sau uku akeyi, wai saboda jama'ah ta yi yawa.

SAHIHUL-BUKHARI, HADISI NA 912-913.

Yanzu kuma su kira biyu suke yi a wannan zamani.

To, idan aka ce sunnar wadannan bid'ah ce wacce ta zama bata/halaka, kuma qarshenta shiga wuta, sai muce zai iya zama hakan, domin su ba Khalifofi bane.

Amma sunnan Khalifofi 12 wadanda Annabi (S.A.W.W)yayi magana a kansu, shiriya ce ba bata ba. Domin umartarmu ma akayi da bin sunnarsu (A.S).

Daga wakilanmu na,Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

           09039791509

~15th April, 2020.  KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post