Billahi alaikum, "Wanda yake ganin shi bazai bada jinin sa ba, to, dama ya ja baya" – Sheikh Zakzaky (H)

*


Ma'asumah Nigerian News Update


Daga Muhammad Altine Bauchi. 

  *Jawabin Sayyid Zakzaky (H). 30/1/1437 Hjr. 12/11/2015. Husainiyyah Bakiyyatullah:*

  "...Mu awurin mu kamar yadda Imam Husaini (as) yake tare da Sahabbai, wadanda yace bai san wasu Sahabbai kamar Sahabban sa ba, irin wadan nan su Hilal bin Nafi'i din nan, wadanda suka ce; "yi damu gabas ko yamma, duk inda kayi muna tare da kai, muna bisa basira kan cewa muna tare da gaskiya ne.

  To irin wannan ne muma zamu dake, saurar (Gwa-gwarmayar) *Imam Husain (as)* abinda ta koyar kenan; nasara ta wata hanyar da ba'a tsammahani, su suna tsammahani da karfin tsiya ne, haukataku da makamai da shi ne ake nasara, billahi alaikum, In mutum yana da hankali ya duba ya gani saboda Allah!, makami aka sa aka tara wadan nan mutanen da kuke gani, fada aka yi, zagi aka yi?!

KARANTA NAN: Wayar da kan jama'a, game daa cutar Coronavirus– Isma Medical Initiatives


*-Hankali da ilimi akasa.* 

 -To amma kuma me ya tattara wan nan jinin; jinin Imam Husaini (as), Jinanen Iyalan sa da na Sahabban sa -me ya tattara mu da su-.?!. 

-Abinda ya tattara su- shi ya tattara mu tare da su, to yanzu sai ana mana barazanar za'a shekar da jini, *billahi alaikum, wanda yake ganin shi bazai bada jinin sa ba, to dama ya ja baya!,* barazanar mutuwa baya karamana komai sai dakewa, saboda haka duk abinda zaku yi kuyi.!

In -da- shawara zamu baku, sai muce kar ku yi kuskuren daukar Matakin karfi, shawara muka baku, amma in kuka kuskure kuka yi, to albishirin ku da hasarar Duniya da lahira, al bishirin ku, zaku tanbatsa Al'amarin ta inda bakwa zato, Kuma wallahi tallahi sai kun yi da na sani!....!"

*_Maulana Allama Sayyid Zakzakiy (H) jawabin sa a Husainiyyah baqiyyatullah_*

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post