Banga Laifin Wanda Yace Zuwan Covid-19, Yana Da Alaqa Da Abin Da Akai Wa Zakzaky Ba





Rbtw: Abba Gano

tabbas akwai buƙatar muyi nazari sosai, don bincike wajen gano silar wannan musiba data addabi duniya.

Naga dayawa cikin ƴan shi'a suna maganar cewar wannan musibar tana daga cikin silar abinda akai wa zakzaky.

To lalle akwai buƙatar muyi nazari cikin maganar tasu don mu gani mene gaskiyar maganar tasu!!!

Idan nace masu wannan tunanin ƙarya suke, saboda zakzaky a Nigeria ne akai masa wannan abin, arhali ita kuma cutar ta shiga sassan duniya, to sai kuma ayar alkur'ni tabani amsar tambaya ta.

( وَاتَّقُوا فِتْنَةً لَّا تُصِيبَنَّ الَّذِينَ ظَلَمُوا مِنكُمْ خَاصَّةً ۖ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ )

الأنفال (25) Al-Anfaal

LATSA NAN👇
☞ ͡Ahkam: Hukuncin Azumin Mace Mai Ciki, Ko Shayarwa
☞ ͡Shin, Har Yanzu Ba'a Sami Irin Waɗannan Malamai Bane??
☞ ͡Kaɗan Daga Cikin Nasihar Da Syed Khamene'i Yayi Wa Shugaba Buhari A 2015

(Kuma ku ji tsõron fitina wadda bã ta sãmun waɗanda suka yi zãlunci daga gare ku kẽɓe, kuma ku sani, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.)

To inde hakane kenan silar hakan yana iya sawa bala'in ya shafi ko'ina tunda suna ji suna gani ake zaluntar wannan bawan Allah !!!

Idan musiba tazo bata ƙyale kowa, tana samun kowa ne, ciki harda muminai, to duk dayake shi mumini tana zamar masa kaffara ne.

Naji waɗan da suke alaƙanta kisan suna cewa, cutar tana da symbol irin na abinda zakzaky ke fama dashi.

Farko tana sanya zaman guri ɗaya' babu zuwa ko'ina, sai kuma naga hakan ga cutar

Sannan tana wajabta sanya takunkumi na baki, canma saina hoton zakzaky da abin baki a bakin sa.

Tana sanya tsaro mai tsanani, sai kuwa naga yanda ake dukan mutane idan suka fito,

To shin meyasa bazamuyi wa wannan bawan Allah adalci ba!!! Shin kawai dan yana shi'a ? To mu ai addinin musulunci yakoya mana adalci kan kowa.

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُونُوا قَوَّامِينَ لِلَّهِ شُهَدَاءَ بِالْقِسْطِ ۖ وَلَا يَجْرِمَنَّكُمْ شَنَآنُ قَوْمٍ عَلَىٰ أَلَّا تَعْدِلُوا ۚ اعْدِلُوا هُوَ أَقْرَبُ لِلتَّقْوَىٰ ۖ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ )

المائدة (8) Al-Maaida

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayin daka dõmin Allah mãsu shaida da ãdalci. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutane ta ɗauke ku a kan bã zã ku yi ãdalci ba. Ku yi ãdalci Shĩ ne mafi kusa ga taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post