@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
FADA (fighting)TSAKANIN 'YAN'UWA BA A SHIGA TSAKANI
Karin magana ce ta malam bahaushe yace ba a shiga tsakanin fadan 'yan'uwa, ma'ana za a iya jin kunya domin za su iya daidatawa.
A koyarwar Ahlul-Bait (A.S)ya kamata ace an sami mabiyinsu (dan shi'ah)ya zama shi yafi kowa tarbiyyah da yin abinda ya kamata cikin al'umma. Hakan kuwa na aukuwa, amma dai ba kowanne dan shi'ah ne amintacce ba.
Abin takaici, sai ka sami dan shi'ah mai amsa sunan mabiyin A'imma(A.S)ne, amma kuma halayyarsa ta sha bamban da koyarwarsu.
Nuna qaunar juna da dinke dukkan baraka da za ta iya haifar da gaba cikin 'yan'uwa na daga cikin manyan abubuwa da jagoranmu Sayyid (H)ke koyar da mabiyansa. Kuma akan haka manyan almajiransa suka doru, kuma suke jaddada wannan koyarwa cikinmu qananan mabiya.
Sai dai duk da haka ana samun masu qoqarin jefa gaba da qiyayya tsakanin 'yan'uwa, wasu kuma su kanyi amfani da wata dama ta hanyar hura wutar fitina da dorewar gaba in sunga wani sabani ya auku tsakanin mutum biyu.
To, ku sani, duk mai irin wannan dabi'a/halayya ya sani cewa wannan ba ita ce koyarwar harka ba, kuma ba halayya ce ta mabiya Ahlul-Bait (A.S)na haqiqa ba.
Wani hadisi na cewa;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ SULHUNTA TSAKANIN MUTANE BIYU YA FI SALLAH !‘’
Wani kuma yana cewa;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ BA ZA KU ZAMA MA SU IMANI BA HAR SAI KUN SO JUNA .‘’
Kunga kuwa Allah ba ya karbar sallar marar imani.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~4th April, 2020.
Tags:
Tunatarwa