An Sake Tsaurara Dokar Hana Fita A Neja Biyo Bayan Barkewar Cutar COVID19 A Jihar

An Sake Tsaurara Dokar Hana Fita A Neja Biyo Bayan Barkewar Cutar COVID19 A Jihar

Gwamnatin jihar Neja a zama da ta kira na gaggawa karkashin jagorancin gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ta sanar da sake tsaurara dokar hana fita a jihar biyo bayan barkewar cutar Corona Virus a karon farko a jihar.

Gwamnan Abubakar Sani Bello ya ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar Litinin har sai in ma sha Allah. Ya ce za a raba kayan tallafin abinci ga unguwar Limawa da aka fara samun bullar cutar domin dokar hana fitar za ta fi tsauri a nan.

Gwamnatin ta sanar da sake dakatar da gudanar da Sallar Juma'a da Ibadun Lahadi da sauran aiyukan ibadu. Har wayau ta bada sanarwar ci gaba da rufe makarntu har sai lokacin da ta ga ya dace a bude su.

A baya dai gwamnatin ta bada umarnin tsagaita zirga zirga daga karfe 8 zuwa 2 na rana sannan ta ba da umarni ci gaba da gudanar da harkokin addinai.

Daga shafin Zuma Time Hausa.
Tare da wakilanmu
Auwal Tukur

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post