Daga Bin Haroun Sigau
Abban ya Ruwaito cewa, yaji daga Sulaym Wanda yace; Naji Ali Bin Abi Talib (As) yace; "Al'umma Zasu rarrabu kashi 73, Kashi 72 zasu tafi wuta sai kashi ɗaya (1) ne za'a wuce dasu aljanna.
Daga cikin 73, 13 zasu nuna soyayyar su gare mu, mu Ahlul Baty wanda su kuma kashi daya zasu tafi aljanna kashi 12 zasu tafi wuta. Qungiya da zasu tsira sune, wadanda aka saka su kan hanyar gaskia suka yi imani, su bi ta da yaƙini, su kai biyayya ga umurnin mu.
LATSA NAN👇
☞ ͡Ahkam: Hukuncin Azumin Mace Mai Ciki, Ko Shayarwa
☞ ͡Shin, Har Yanzu Ba'a Sami Irin Waɗannan Malamai Bane??
☞ ͡Kaɗan Daga Cikin Nasihar Da Syed Khamene'i Yayi Wa Shugaba Buhari A 2015
Su ne wanda suka aminta dani, sukayi biyayya gare ni (Imam Ali), suka zabi ƙaurace wa maƙiya na, suka so Ni, suka ci gaba da kiyayya da maƙiya Na, suka fahimci gaskiyar Imaman ci Na, sannan suka fahimci tsantsar biyayya ta zuwa ga littafin Allah (swt), Allah ya haskaka zuciyarsu da ilimin sanin haƙƙin Mu.
Kuma suka san Muhimmancin Mu, kuma dukkan waɗannan ya nutse a cikin zuciyar su kuma rubuce a goshin su. Allah (swt) ya saka su cikin ƴan Shi'a ta, har sai da zuciyar su ta gamsu, ta tabbatar masu ba tare da yin kokon to ba."
Madogara: Kitaab Sulaym Ibn Qays Al-Hilaali, Hadisi Mai Lamba 7.
KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN