@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
AKAN ME MUTUM YA MUTU BA WAI AKAN ME YA RAYU BA
Sau da yawa mutane na shiga cikin rudu idan suka ji an ambaci wata kalma marar dadin ji ga wani, wanda su a tunaninsu mutumin kirki ne.
Lalle irin wannan tunani ba daidai bane, domin an riqa samun wadanda suka yi mummuniyar rayuwa a tarihin muslimci, amma kuma sai su kayi kyakkyawar makoma a qarshen su. An samu da yawa daga cikin kafirai wadanda suka dawo cikin musulmi a lokacin yaqoqi kuma su kayi shahada.
Baghwiy yace; Aliyu dan Ja'ada ya bamu labari, Abu Gassar Muhammad Bn Mudrafi Al-Madniy ya bamu labari daga baban Hazeem, daga Sahal Bn Sa'ad yace;Manzon Allah (S.A.W.W)yace;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ Lalle bawa zai iya yin aiki wanda mutane na gani aiki ne na 'yan Aljannah, alhali kuwa shi dan wuta ne. Kuma shi (bawa)zai iya yin aiki wanda mutane na gani aiki ne na 'yan Wuta, alhali kuwa shi yana daga 'yan Aljannah. Shi dai aiki yana daga cikawa ne (halin da mutum ya mutu a ciki).‘’
(Bukhari, J:8, SH:155).
Saboda haka bai zama abin mamaki ba don ka ji ance wasu sunyi riddah, wasu kuma sun tabbata !
KU KARANTA NAN👇
☞ ͡Ku tambaye ni kafin ku rasa ni Fita Na Ɗaya (1)
☞ ͡Du'a Muqatil| Addu'ar biyan bukata da gaggawa
☞ ͡Wallahi akwai maganin Covid-19 a Najeriya Ku tambayi Zakzaky –Inji Wani Bawan Allah
ALLAH (T)NA CEWA;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ WASU JAMA'A MUN SHIRYAR DASU WASU KUMA BATA (halaka) TA TABBATA , DOMIN SU SUN RIQI SHAIDANU (a matsayin)MASOYA KOMA BAYAN ALLAH, KUMA SUNA TSAMMANIN SU SHIRYAYYU NE !‘’
(A'ARAFI, AYA TA 30)
Wato su wadannan batattun da shaidanun da suka riqa suna tsammanin sune shiryayyu koma bayan muminai.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~17th April, 2020.
WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Taskar ilimi