Ahkam: Hukuncin Azumin Mace Mai Ciki, Ko Shayarwa






@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

AMSA DAGA FATAWAR SAYYID KHAMENE'I

TAMBAYA:- Shin, mace mai cikin da bata san ko azumin nata zai cutar da jaririn nata ko kuma a'a ba, wajibi ne tayi azumi?

AMSA:- Idan har tana tsoron cewa azumin zai cutar da jaririn nata kuma tsoron nata yana da tushe na masu hankali, to, wajibi ne ta sha ruwa, idan kuwa ba haka ba, to, wajibi ne tayi azumi.

DANNA NAN👇
☞ ͡Nine El-Zakzaky, Babban Wanda Aka Fi Zalunta
☞ ͡Yaa Ubangiji! Kurkuku Ne Mafi Soyuwa Daga Abinda Suke Kirana Zuwa Gareshi
☞ ͡Jahili ne Kaɗai, Ke Murna Da Kisan Kiyashin Da Akai Wa Ƴan Shi'a

TAMBAYA:- Ni na kasance mace mai shayarwa ce bayan da Allah ya azurta mu da yaro, kuma ga shi watan azumi ya gabato, amma a halin yanzu ina iya yin azumi, to, amma a duk lokacin da nayi azumi ruwan nonona yakan qafe don ni mai raunin jiki ce, kuma wannan da nawa yakan buqaci a duk bayan mintuna goma, to, yaya zan yi?

AMSA:- Idan har wannan qafewa da ruwan nonon naki yake yi a sanadiyyar azumi, kuma kinji tsoron zai cutar da jaririn, to, ya halatta ki sha ruwa, amma za ki dinga bayar da mudu guda na abinci ga faqirai a kowacce rana, bugu da qari kan rama azumin da za kiyi daga baya.

(ma'ana, za ta iya ajiye azumin nata, amma za ta riqa ciyarwa, sannan daga baya za ta rama azumin data sha).

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

         09039791509

~27th April, 2020.

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post