A Yau Laraba ne tawagar Taliban ta isa birnin Kabul a karon farko da aka kifar da gwamnatinta a 2001 domin haduwa da gwamnatin kasar.
(ROHOTON ABNA24.com) Kakakin majalisar koli ta tsaron kasar Afghanistan Jawid Faisal ya rubuta a shafinsa na; Twitter cewa; Gwamnati ta karbi bakuncin tawagar ta Taliban inda aka bude tattaunawar kai tsaye akan musayar fursunoni.
Jawid ta kara da cewa; wakilan kungiyar agaji ta “Red Cross” ta halarci tattaunawar ta yau.
A nashi gefen, kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya ce; Tawagar tasu ta tattauna da jami’an gwamnati akan hanyoyin musayar fursunoni.
Batun sakin fursunoni yana cikin yarjejeniyar da aka kulla a tsakanin Taliban da gwamnatin Amurka, wacce kasar Qatar ta shiga tsakani
Tags:
Labaran Duniya