Addu'ar biyan buqata da gaggawa!






@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DAGA IMAM ALIYU ZAINUL-ABIDEEN (A.S)

Wannan wata addu'ar tawassuli ce ta Imam Sajjah (A.S)wacce ake kiranta da addu'ar Muqaatil Bn Sulaiman.

Muqaatil Bn Sulaiman yace, duk wanda yayi addu'a da wannan addu'ah sau dari (100)amma ba a amsa masa ba, to, ya la'anci Muqaatil.


KU KARANTA NAN👇
☞ ͡Ku tambaye ni kafin ku rasa ni Fita Na Ɗaya (1)
☞ ͡Wallahi akwai maganin Covid-19 a Najeriya Ku tambayi Zakzaky –Inji Wani Bawan Allah

Ga addu'ar nan kamar haka;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ ILAHEEY ! KAIFA AD'UKA WA ANA ANAH? WA KAIFA AQDA'U RAJAA'IY MINKA WA ANTA ANTA ?

ILAHEEY ! IZAH LAM AS'ALUKA FA TU'UDEENIY, FAMANZALLAZEEY AS'ALUHU FA YU'UDEENIY?

ILAHEEY ! IZAH LAM AD'UUKA FA TASTAJEEBA LIY, FAMANZAL-LAZEEY AD'UUHU FA YASTAJEEBA LIY?

ILAHEEY ! IZAH LAM ATADHARRA'U ILAIKA FATAR-HAMUNIY, FAMANZAL-LAZEEY ATADHARRA'U ILAIHI FAYAR-HAMUNIY?

ILAHEEY ! FAKAMAH FALAQTAL-BAHRA LI MUSA ALAIHISSALAAMU WA NAJJAITAHU, AS'ALUKA AN TUSALLIY ALAH MUHAMMADIN WA AALIHI, WA ANTUNAJJIYANIY MIMMAH ANA FEEHI, WA TUFARRIJA ANNIY FARAJAN AAJILAN GHAIRA AAJILIN, BI FADHILIKA WA RAHMATIKA YAA ARRAHMAR-RAAHIMEEN .‘’

‘’ (Allah)Abin bautana ! Ta yaya ba zan kira ka ba alhali nifa nine (bawa qasqantacce)?Kuma ta yaya zan yanke tsammani daga gare ka alhali kaifa kaine (Allah mai iko)?

Abin bautana ! Idan har ban roqe ka ka bani ba, to, wa kuma zan roqa (koma bayanka)ya ba ni?

Abin bautana ! Idan har ban kira ka ka amsa min ba, to, wa kuma zan kira (koma bayanka)ya amsa min?

Abin bautana !Idan har ban qasqantar da kaina gare ka (don girma da isarka)ka tausaya min ba, to, ga wa kuma zan qasqantar da kaina gare shi (koma bayanka)wanda zai tausaya min?

Abin bautana !Kamar yadda ka keta/tsaga Teku ga Musa aminci ya tabbata a gare shi (yayin da Fir'auna ya bi shi)ka tseratar da shi, to, nima ina roqonka da kayi salati ga Muhammadu da Iyalansa, kuma ka tseratar dani daga abinda nake cikinsa (na damuwa ko qunci ko rashin lafiya d.s), kuma ka yaye min shi cikin gaggawa ba bisa jinkiri ba, domin falalarka da tausayawarka (ba don halina ba), yaa mafi tausayin masu tausayi .‘’

(MAFATIHUL-JINAAN, gaba kadan da DU'A'UT-TAWASSUL)

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

09039791509-08126385470

~15th April, 2020.



 KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post