A Zamanin Nan Banga Irin Sheikh Zakzaky Ba, _Inji Abba Gano






abbagano✍️

Bara mufara saka aya ta tabbatar mana da cewar matsayin da zakzaky yake kai, masu matsayin ne sukafi kowa ɗaukaka da girman daraja, agun Allah.

Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin Allah, (shĩ ne) wanda yake mafĩfĩcinku a taƙawa.

13) Al-Hujuraat

Duk tarin yawan mutane, komi matsayin su da dukiyar su, mai taƙawar cikin su shine yafi kowa matsayi a gurin Allah!!!

Alamomin masu taƙawa Allah ya anbata a Alkur'ani dayawa, amman zamu ɗau biyu.

1= Dogaro ga Allah!!!

Tabbas Sayyid zakzaky dogaron sa Allah ne, hakan ne ma yasa duk abinda yasame shi sai yayi hakuri ya daure domin yasan jarrrabawa ce.

Lokacin da azzalumai suka afka masa a shekarun baya, lalle su Sayyid sun faɗi irin abinda Annabi Musa yafaɗi ne lokacin da far'auna ya sako shi gaba zai kashe shi!!!

{"Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni."}

62) Ash-Shu'araa

Sayyid haka shima ya dogara ga Allah ya zauna cikin gidan sa har abinda ya same shi ya same shi!!!

2= "Hakuri akan musiba."

Lokacin da ɗan Annabi ƴakub ya bata, haka yayi ta kuka har ya makance, duk da yasan zai dawo gareshi tunda annabin Allah ne shi.

Amman zakzaky ƴaƴan sa 6 aka kashe, wasu ma agaban sa, amman shi dakan sa yake faɗawa ƴan uwa ayi haƙuri.

Su Sayyid a ƙalla sau 10 ana sanya su gidan yari, (prison) duka saboda addini, kuma su Sayyid sunyi hakuri bisa hakan.

Yana daga haƙuri makashin ƴaƴan ka yazo ya miƙa maka hannu ku gaisa, kuma kabashi hannu.

Lokacin da makashin Imam Ali yazo kashe shi a masallaci, dakan sa,Imam ya tashe shi abarci yace masa lokacin aikin ka yakusa.

Su Sayyid ma haka suke iya hannu da maƙiyan su, su tarbi makasan ƴaƴan su, da abinci da ruwan sha.

{ manyan darajoji suna ga manyan bala'o'i,}

 sai na'auna kaf yanzu babu wanda aka zalunta kamar zakzaky, kenan darajar sa sai tafi ta kowa, tunda babu wanda yakai shi a yawan bala'o'i a Yanzu.

{"Kuma lalle ne, Muna jarrabar ku da wani abu daga tsõro da yunwa da naƙasa daga dũkiya da rãyuka da 'ya'yan itãce. Kuma ka yi bishãra ga mãsu haƙuri."}
 البقرة (155) Al-Baqara

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post