ziyarar mu gasu malam muhammad kabir imam malumfashi a kurkuku


wakilin yan uwa nagarin malumfashi mlm mhmd kabir imam mlf





   A yau Talata 3/3/2020 ne aka ziyarci Wakilin 'yan uwa almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na garin Malumfashi, Malam Kabir Imam malumfashi da wasu 'yan uwa uku, Husaini Almustapha, Muntari Musa Nababa da kuma Kamaladdeen Musa Nababa wadanda ake tsare da su a gidan kurkuku dake cikin garin Katsina bisa zalunci na Azzaluman mahukunta Nijeriya.
   A yayin ziyarar, bayan gaisuwa da Malam Kabir Imam da sauran 'yan uwa uku. Malam Kabir Imam ya bayyana mana irin matsanancin halin rashin lafiya da yake fama da shi a inda ake tsare da shi, wanda a halin yanzu yana samun sauki cikin ikon Allah ta'ala.

   Haka zalika, a yayin ziyarar mun samu tabbacin cewa bayanan da ake yadawa na cewa jiya Litinin 2/3/2020 babban mai rawani na garin Malumfashi da wadansu manyan gari sun je wurin da ake tsare da su Malam Kabir Imam sun gana da shi na tsawon lokaci karya ce tsagwaronta. Babu wani abu mai kama da haka da ya faru. Babu wadansu manyan gari da suka je wurin Malam Kabir Imam ballantana su tattauna da shi.

   Ana tsare da Malam Kabir Imam ne tun ranar Juma'a 21/2/2020 biyo bayan dirar mikiyar da jami'an tsaro 'yan Sanda suka yi masa a gidansa haka siddan, suka kama shi suka tafi da shi da 'yan uwa uku suka tsare su bisa zalunci.

   Bayan 'yan Sanda sun gurfanar da su a gaban Kotu a ranar Talata an karanta masu laifin da ake tuhumar su da aikatawa wanda suka musanta aikata shi. Nan take kawai sai aka wuce da su zuwa gidan yari dake cikin garin Katsina da nufin cewa ranar 6/4/2020 za a ci gaba da shari'a.
   Hakika Malam Kabir Imam ba shi da lafiya a halin da ake tsare da shi. Don haka muna addu'a Allah ta'ala ya kara inganta lafiyar Malam Kabir Imam, ya zama gatansu ya kuma daukar mana fansar bakin zaluncin da ake yi masu.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post