Zazzaɓin lassa da hanyoyim kariya




Daga: M.N.N updates

Tareda: Jibril Usman Sarki (08149953832)

Shi zazzabin lassa wani irin zazzabi ne da kwayar cutar Virus kankawo.Ana samun cutar ne ga beraye yayin da sukan jefata ga al'umma.

Beraye sukan yi yawo a gidajenmu su je neman abinci musamman da dare. Wasunsu a irin wannan lokaci sukan kwaso wadannan kwayoyi na virus. Wasu sukan hauro ta katanga, wasu sukan shigo ta rariya, wasu kuma ma suna da ramuka cikin gidajenmu. Idan suka taba abincin da yake a bude, sukan iya sa mana wadannan kwayoyi abinci, mu kuma mu dauka in mun ci. Wasu lokuta ba sai sun taba mana abinci ba, kashinsu da fitsarinsu kan iya yada kwayoyin cutar ta hanyoyin numfashi idan muka shaki warin.

Ana kuma iya daukar ciwon ta hanyar taba jikin mai ciwon, musamman a ma’aikatan asibiti.

Alamomin ciwon

Akwai zazzabi, sai ciwon ciki da amai da gudawa, wadanda za a iya ganin jini a ciki. Babu inda ciwon bai iya tabawa, domin za a iya jin kasala, ciwon kai, tari, mura da dai sauransu. Don haka babu dai takamaimai wata alama guda daya da za a danamai

a ciwon da shi.

Hanyoyin Kariya
1. Kada a rika bari beraye suna samun sukuni a cikin gidajenmu; a nemi ramukansu a tottoshe musamman a dakunan da ake ajiyar abinci wato store; a kuma kawo mage cikin gidan.

2. A daina barin abinci a bude ko da yaushe ya zama a rufe, kada wani abu ya shiga

3. A daina barin kwanukan abinci suna kwana ba wanki. Mun san yawancin gidajenmu akan bar wanke-wanken kwanuka zuwa da safe, wanda hakan kan iya jawo beraye su hau kwanukanmu cikin dare. Ko da an yi wanke-wankenma, a dauraye su sosai kafin a zuba abinci

4. Idan an yi wanke-wanke a share guntattakin abinci sosai, kada a bari su shiga rariya, don gudun kada ya jawo beraye.

5. Idan an ga fitsari da kashin beraye kada a share sai an sa kyalle an rufe hanci tukuna

6. Idan an ji zazzabi da ya wuce kwana biyu, ko ya ki jin magani, a garzaya asibiti

7. Idan ana da maras lafiya wanda ake tunanin yana da wannan ciwo, kada a rika taba shi sosai ko amansa, a sa leda a hannu kafin a yi aikin amai

Sanan agaggauta kai Wanda ykedauke da chutar asibiti domin bashi kulawa cikin gaggawa.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post