Zazzabin Lassa Ya Kashe Basarake A Bauchi.

A Lokacin Da Hankali Ya Karkata Ga Ciwon Coronavirus Lassa Kuma Ta Kai Basarake Kabari.

 Daga -Idishia Jos


A ranar Juma’a ne cutar zazzabin Lassa ta yi ajalin Basaraken Gargaji a Bauchi wato Katukan Bauchi, Injiniya Garba Adamu wanda kuma shine Hakimin Kasar Toro. Wakilinmu ya labarto cewar a lokacin da aka tabbatar da cutar ce ta rufke Basaraken, jami’an kiwon lafiya sun yi kokarin ceto rayuwarsa ta hanyar killace shi a asibiti na musamman da bashi kulawa ta musamman a Abuja amma lamarin ya ci-tura.


Makasudin mutuwar tasa ta fito balo-balo ne a ziyarar neman agaji da gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir ya kai wa Darakta Janar na cibiyar dakile yaduwar cutuka ta kasa National Center for Disease Control (NCDC) da ke Abuja a jiya. Gwamnan ya kuma shaida cewar yanzu haka akwai wasu jami’an kiwon lafiyan da ake zargin sun kamu da cutar ta Lassa don haka ne ma aka kebesu domin samar musu da kulawa da shawo kan cutar.


A cewar gwamnan, “A sakamakon barkewar cutar Zazzabin Lassa a jihar Bauchi wacce har ta jawo mutuwar Hakimi da kuma kamuwa da ita cutar da wasu jami’an kiwon lafiya suka yi. “Bana da wani zabi da ya wuce na hanzarta dakatar da ziyarar aiki da na kai kasar Jamani domin na gaggauta zuwa neman tallafi daga wajen gwamnatin tarayya ta hannun DG na hukumar dakile yaduwar cutuka da kuma hukumar lafiya tun a matakin farko ta kasa (NPHCDA),”


Wakilinmu ya nakalto cewar marigayi Katukan Bauchi, Garba Adamu Toro dai Mai martaba Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu ne ya nada shi Hakimin Kasar Toro a ranar 8 ga watan Disamban 2019 da aka yi wa wankan nadin Sarauta a ranar 22 ga watan Fabrairun 2019.


Ya rasu ne a ranar 13 ga watan Maris na 2020 a babban asibitin kasa da ke Abuja sa’ilin da ke amsar kulawar likitoci. An kuma yi masa jana’iza da kaishi makwancinsa a ranar Asabar a karamar hukumar Toro.



Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post