Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da wasu yan kasar China su biyu
An tattaro cewa an sace mutanen ne a karamar hukumar Ivo da ke jahar
Rundunar yan sanda ta tabbatar da lamarin yayin da ta ba da tabbacin ceto su ba tare da bata lokaci ba
Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da wasu yan kasar China su biyu da ke aiki a jahar Ebonyi a ranar Litinin, 30 ga watan Maris.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an yi garkuwa da mutanen ne a yankin karamar hukumar Ivo da ke jahar.
An gano cewa wadanda aka sacen sun kasance masu aiki a wani kamfanin sarrafa ma’adinai a yankin.
An tattaro cewa kwamishinan yan sandan jahar Ebonyi, Awosola Awotide ya tabbatar da lamarin.
Ya bayar da tabbacin ceto mutanen biyu ba tare da jimawa ba, inda ya ce rundunar ta bi sahun masu garkuwan.
By Bin Haroun Sigau
Tags:
Labaran Duniya