Yanzu mu muna fuskantar wani irin nau'in yaki ne –Sheikh Zakzaky (H)

Sayyid Zakzaky a shekarun baya

MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE


–Bin Haroun Sigau

To, yanzu mu muna fuskantar wani irin nau'i na yaki, yaki wanda yake ya fi yaki a yake ka da Takobi Yanzu yakin ana yakar ka ne da tunani. Ana yakar tunaninka ne, ana so kai ka zama kana Musulmi, amma kana tunani wani iri daban. Har ma na ga irin wannan da suka je suka yi wannan barnar a Mali. Mu a nan Musulunci ya zo nan bangaren ta Mali ne. A Mali na ga ana hira da wasu a Talabishin, na gani ne ana nunawa, sai aka ce, wadansu wanda ake ce musu ko Ansaruddin ne? Wadanda suka je suka kama Birnin Timbuktu, suka takura ma mutane. To, sai ana hira da su, to ku su wene ne? Sai suka ce wai su suna son a yi shari'ar Musulunci ne. Sai suka tambayi mutanen gari cewa; to, ku kuna son Shari'a ne? Sai suka ce, ba mu so, domin ana tattakura wa mutane. Ka ga mutane ba su san me ye ma'anar sharı'ar Musulunci ba, sun dauka tursasa ma mutum da takura shi shi ne shari'a. Alhali shari'a tana nufin hanya, hanya tiryan-tiryan ya zuwa mafita, wanda za ka bi ka tsira. Amma zare ma ido, a daka maka Tsawa, a zaro takobi a gigara maka a wuya a ce, Shari'a.

Har ma 'yan Kudu sun dauki ma'anar Shari'a din a wajajen, tun ba kasashen Ibo ba, idan aka kama barawo, sai ka ji suna ce masa; 'shari'a him, shari'a him.' Sai su gutsire masa hannu. Sai su samo guduma su kwankwatsa hannun, wai sun yi masa shari'a kenan. Wato ainihin ana neman a canza ma'anar addinin ya zama wani abu daban. Kalma mai kyakkyawar ma'ana, duk an maishe su munanan ma'ana. Hatta makarantunmu an maishe su wuraren abin tsoro. Hatta idan yaro yana karatun Alkur'ani yana dan kada kan nan, sai a nuna a ce; ka gani, dan ta'adda kenan, ka ga yana wani haka, zai ta da hankali ne. Idan kun lura a Talabishin, ku rinka kallo, idan kuna kallon Talabishin, za ku ga cewa; idan suna ba da labarin 'yan ta'adda, to sai ka ga a bayan labarin ana magana sai a nuna mutane suna sallah; ka ga sallah mene kenan? Yawwa! Sai kuma su nuna mata da hijabi; to, ka ga hijabi mene ke nan? Sai a nuna wani da Tasbih; to, mene kenan yake nufi? Sai a nuna wani da Rawani; Rawani mene kenan? Sai a nuna Masallaci; Masallaci mene kenan? Sai a nuna ana dawafi a Ka'aba, amma ana ba da labarin an yi ta'adda ne. Wato suna son duk lokacin da mutum ya ga wadannan ya tuna da ta'addanci. Saboda haka ya zama addinin Musuluncin an canza masa ma'ana.

–Sheikh Zajzaky (H), a taron tuna haihuwar Manzon Allah (S) ranar talata, 1 ga watan Rabi'ul Auwal 1436.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post