yanda ake anfani da:madara wajen magancebmaiqon fuska.




Ma'asumah Nigeria News Update.

M.N.U.030



Shan madara na kara lafiyar jiki, tana sanya fata ta rika sheki, ta sanya ta yi taushi da kuma santsi. Hakan ya sa a yau shafin ma'asumah Nigeria News Update ya kawo muku yadda ya kamata ku yi amfani da madara wajen magance yawan maikon fuska.

Abubuwan bukata

Madara
Gishiri
 Ruwa
Auduga
Zuma

Amfanin madara wajen magance maikon fuska

1. Madara na goge daudar fuska: A samu madara rabin kofi, sannan a hada ta da rabin cokalin gishiri, sai a sanya ruwa a gauraya har sai gishirin ya narke. Daga nan a shafa a fuska da wuya zuwa minti 2 ko 3 kafin a wanke da ruwan dumi.


2. Madara na sanya fata santsi: don haka za a iya amfani da ita a matsayin sinadarin ‘cleanser’. Da farko a samu auduga, sai a tsoma a cikin madarar ruwa, daga nan a rika goge fuska da ita. Daga nan a jira ta bushe kafin a wanke.  Yin hakan na rage maikon fuska, kuma zai sanya fuska ta yi taushi da santsi.


3. Za a iya amfani da madara don kara wa gashi karfi: musamman lokacin sanyi da gashi yakan tsinke. A zuba madara a kan gashi a cuda har ta taba tsagun kai, sai a jira na minti kadan kafin a wanke. Yin hakan na kara karfin gashi kuma yana hana shi tsinkewa.


4. Za a iya hada madara da zuma sannan a shafa a fuska. Yin haka na hana tsagewar fatar fuska saboda sanyi.


Wakilanmu na kano Sakina Ahmad & shaheder fertymerh

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post