Yana da shekaru 27 ya tarwatsa arnan Badr!!



@ MA'ASUMAH NUGERIAN NEWS UPDATED @

GARE KU MATASAN HARKA

Yaqin Badr ya kasance yaqi na farko a muslimci (it is the first physical combat between muslims and Pagans)wanda aka fara shi ranar 17 ga Ramadan cikin shekara ta 2 bayan Hijra (B.H).

Dalilin wannan yaqi shine, kafiran Makkah sun kasance suna tare hanyoyi ne suna karbe dokiyoyin fatake musulmi masu yin fatauci tsakanin Makkah zuwa Madinah . Suna qoqarin karya tattalin arziqin musulmi da muslimci da ke dagowa. Wannan dalili yasa Allah (T)ya umarci musulmi da cewa su fito su yaqe su.

Abu Sufyan ne ya jagoranci rundunar kafirai da ke dauke da mayaqa 1000, yayin da Annabi (S.A.W.W)ya jagoranci musulmi wanda adadinsu shine 313.

Utbatu Bn Rabi'a da dan'uwansa Shaibata da dansa Walid ne suka fito gaban Manzon Allah (S.A.W.W), yadda Utbah yake cewa;

‘’ YAA MUHAMMAD ! KA FITO MANA DA SA'ANNINMU,DAGA QURAISHAWA !‘’

Jin haka sai wasu matasa 3 daga matasan garin Madinah (ANSAR)suka fito don tinkararsu, amma bayan sun bayyanar da kansu gare su sai Utbatu yace ba sa buqatarsu, sun fi son 'yan'uwansu na Makkah su fito.

Sai Manzon Allah (S.A.W.W)ya cewa wadannan matasa su dawo zuwa wajen zamansu, sannan yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ MIQE YAA ALIYU, KAIMA HAMZA KA MIQE DA KUMA KAI UBAIDULLAHI !‘’

Wadannan mutane uku (3)ne suka fara fuskantar kafirai bisa umarnin kwamanda (S.A.W.W).

Anyi ittifaqi cewa a wannan yaqi an kashe kafirai 70, kuma aka kama 70 daga cikinsu a matsayin fursunonin yaqi.

Abin burgewa da ban sha'awa anan shine, shekarar Imam Ali (A.S)a wannan lokaci 27 ne, amma shi kadai ya kashe mutane 21 daga cikin 70 din da aka kashe.

‘’ HAQIQA ALLAH YA TAIMAKE KU A BADR, ALHALI KUWA KUNA MAFIYA RAUNI.....‘’

    (BAQARA, AYA TA 123)

This is the first military encounter between islam and kufr.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

          09039791509

~14th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post