MAFITA ZUWA IYAYE :: YADDA ZAN AURAR DA DIYA TA, IDAN ALLAH YA RAYANI



Nazari akan rayuwar mu ta yau (wannan rubutu yana bukatar karantawa da nazari ga kowa)

Nayi wannan rubutu ne duba da yanayin da muke ciki kan harkar da ta shafi aure musamman anan kasar Hausa, ganin yadda sabbin al'adu suke kara kunno kai suna hana samari yin aure, suna hana yan mata samun mazaje. Yasa naga ya dace in rubuta wannan makala wala'allah ko mun fa'afa!(Lura)

Sanin kowa ne aure sunnar annabin mu ce (s.a.w) mai karfi, kuma Allah ya halicci maza da bukatar mata haka suma mata an halicce su akan bukatar maza, to amma kirkirarrun al'adu musamman sabbi suna kokarin murkushe auratayya a yanki na na arewa.

Kiyasi da bincike ya nuna cewa a yanzu haka idan ko wane namijin daya isa aure zai auri yan mata biyu ko zawara sai anbar wasu a kasa ba tare da samun mazaje ba. To amma inaaa!! Abin baya yiwuwa kuma gaya kullum kara haihuwar yara mata akeyi, mutum.zai sha mamaki idan aka taso daga makaranta ko kuma ana bukuwa duk inda ya kalla yarane yan mata firda firda masu bukatar mazaje, miyasa bazamu hankaltaba?

Akwai samari da dama masu sana'oin hannu da masu kananan jari da zasu iya rike mace tare da daukar dawainiyarta ta yau da kullum, a matsayin ma'aurata to amma basu da makudan kudaden da ake bukata wajan gudanar da shidimar auren zamani, dole suke hakura sunaji suna gani, mi zai sa bazamu lura mu gane ba?

Yakamata mutane su tashi tsaye wajan gyara a cikin al'umma matukar abin da bai fi karfinsu bane ko kuma bai Shiga hurumin hukuma ba, domin akwai abubuwa da yawa da zamu iya gyarawa da kan mu idan muna bukata, daga daidayakun mu, a hankali sai abin ya zama gama gari, misali a nan garin Daura a shekarun baya ba'a sa ranar aure ba tare da ankai kayan laife ba, kuma ba'a sa ranar aure ta wuce wata uku zuwa hudu, duk Wanda yayi haka yayi abin kunya abin fadi da surutu, amma yanzu gaya abin ya canza, wani Auren ma sai satin biki ake kai kaya, sa ranar aure kuwa yanzu har shekara daya ana sawa, daga bisani kuma a sake kara kwanaki ko watanni.

A halin da muke ciki yanzu auren buduruwa ga saurayi a talauce daga kai toshi zuwa Daura aure, a kalla ana kashe naira dubu Dari uku, a talaucen talauce kenan indai cikin birni ne ba kauye ba, misali:-

1.Toshi - #10'000
2.Sa rana. - #5000
3.kayan lefe. #120,000
4.shidimar biki - #105,000(komai da koma)
5.Kudin haya. - #50,000
6.Sadaki -#20,000
Total. - # 300,000.

Wannan a karshen talauci kenan ga Wanda baya da gidan kansa, Wanda ke da gidan ma sai ya kashe haka, saidai abin lura anan a ina zai samu wadannan kudaden? Yaushe zai Tara su da karamar Sana'a? Gaya kuma ana son auren.

A haka za'a tunkari auren cikin bakar wahala wani lokacin da bashi da rigingimu Wanda za'a Dade bayan aure ba'a warware ba. Maimakon anyi sure ango ya huta sai wata sabon tashin hankalin ya kunno kai na biyan bashin da ba kudin biyan. Cikin wata tara matar ta haihu ga biyan kudin hayar gida, ga dawainiyar suna shi kenan an afka kalubalen rayuwa.

Ita kuma mace a talauce da karamin kafi idan iyayenta zasu aurar da ita sai sun kashe mata dubu dari uku zuwa da hamsin a talaucen talauce, misali:-

1.Idan za'akawo laife - #10,000
2.Tuyar biki. - # 10'000
3.kayan kicin. - # 30,000
4.Gado da kujeru - #200,000
5.Katifa fulo,labulaye. - # 40,000
6.kayan aikin tsakar gida. - # 10,000
7.Garar abinci da atamfa - # 50,000

Total. - # 350,000.

Wannan a karshen talauci kenan kuma wallahi zaka samu da yawa iyayen a gidan haya suke, wasu kuma basu da sana'ar samun naira dubu a kullum, ga iyali, zaka tarar wani diyansa yan mata biyu wani uku wani hudu kai har da mai biyar duk sun isa aure, idan an kukuta an samu da kyar da jibin goshi an saida gona anyiwa ta farko sauran kuma yaya za'ayi dasu, ya Ilahi yaya za'a a zauna lafiya a wannan hali?yakamata mu dawo cikin hayyacin mu.

A haka fa ake bukukuwan mu cikin bakar wahala namiji da iyayensa sai karfi ya kare bare kuma bangaren mace, duk sai kowa ya FIFA daga hayyacinsa saboda tsabar wahalar da kawuna, idan za'a kai kayan laife sai anyi tuya da abinci da lemu Wanda za'a ba yan kawo kaya a nemi kudin da za'a dora na bude akwati, idan ango ya doro dubu goma a kara masa dubu goma su zama ashirin, wajalar banza da wofi, bayan daurin aure za a sai atamfofi da shadda tare da kulolin abinci a rabawa dangin miji kuma a sayi kayan abinci a ba mijin, anya kuwa muna so mu zauna lafiya?

GA MAFITA, YADDA ZAN AURAR DA DIYATA INSHA ALLAH.

Ita dai sabgar aure a hannun uba take matukar uban yasan hakkin dake kansa, idan ko hakane ni zan tsara yadda zan aurar da diyata ba wani ba, ko wasu. Zan zaunar da iyalina da dangimu baki daya in fahimtar da su illolin wannan wahalar da yadda ake jefa kai cikin kunci da takura har mu fahimci juna, don haka sai in fada musu yadda zanyi auren diyata. Idan kuma wani yace a'a bai yarda ba, ko uwar yarinya, shikenan an hutar dani, sai ince to ya kawo dukkan kudin da ake bukata. Idan kuma baya iya badawa to yasa ido yayi kallo.

Shi kuma yaron dayace yana son diyata bayan na tabbatar da tarbiyar sa da sana'ar sa komai kankantar ta idan dai mai dorewa ce, shima sai in kirawo sa tare da magabatan sa muzo muyi zama, in fadamusu tsarin da nakeso yadda bazamu takurawa kawunan mu ba, misali:-

1.Bana bukatar kudin Toshi,
2.Bana bukatar sa ranar biki wadda za'a tara mutane,
3.Bana bukatar kayan laife.
4.Abin da kawai nake bukata shine sadaki Wanda bai wuce naira dubu talatin ba idan ace yanzu ne zan aurar da yarinyar. Bayan aure hakkinta ya koma kan mijjnta duk abin da yake so na sutura da kayan shade shafe sai yayimata a gidansa.

Sai ni kuma in fada musu abin da zanyi musu shine kayan daki Wanda zan saiwa diyata kuma nata ne, bana ango ba, zanyi gwargwadon iko na yadda zan iya, daga nan babu abin da zanyiwa ango ko danginsa.

In tabbatar musu da cewa muna iyabin waccan hanyar mai wahala da ake bi koda kuwa zamuje ne cikin tsanani amma bazan bi ba, don haka idan kun yarda kun amince a haka za'ayi bikin diyata. Idan mun aminta a haka shikenan. Idan kuma basu yarda ba sai inyi mata addu"ar Allah kawo mata wani mijin.

SHAWARA.

Ina mai ba iyaye shawara musamman maza tare da samari da yan'mata su jarraba wannan hanyar kuma kowa ya tsarkake niyyar sa akan haka, da sannu sai abubuwa su sauwaka, ta yadda za'a rage yawan yan'mata da samari babu aure. Amma matukar muka kiya mukace wadannan Sabin al'adun zamuciga dayi munaji muna gani aurar da diyan mu zai gagara, kuma shaidanci da badala zasu cigaba da afkuwa cikin al'umma.

Kada mutum ya damu da surutan mutane, yan uwa ko makwafta da abokai, kawai ya nemawa kansa mafuta, na tabbata da sannu za'ayi nasara akan wannan hanya saboda yanzu ruwan yakai ga wuyan kowa. Mafuta ake nema da wani ya fara wani zai bishi. Kamar yadda suna a kofar gida ya gagara a ka daina saboda tsaraba, shima wannan a haka zai zama gama gari.

Daga karshe ina fatan Allah ya tabbatar Mani da wannan kudiri nawa, yasa shawarar nan ta shiga zukatan mutane, tare da aiwatar da ita, ta yadda wata rana za'a tunani a matsayin Wanda ya kawo canji na alkhairi ga al'umma.

Wanda ya yarda ya huta Wanda kuma ya kiya don Kansa. Ba lalle ba dole nidai haka nake fatanyi insha Allah.

Musa Ibrahim Daura
7-3-2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post