Yadda Cutar COVIC-19 Take da Yadda ake Rigakafinta



Binciken Kwararrun Likitocin China
Wasu Kwararrun Likitocin China sun gudanar da bincike a kan yanayi da dabi'ar cutar Corona a jikin dan Adam sai suka gano cewa, cutar tana shiga cikin jikin mutum ne ta hanyar baki da maqogwaro sai ta isa ga huhu inda za ta fitar da wani kaki mai kauri sosai wanda zai rufe hanyoyin shigar iska. Wato a taqaice dai, cutar tana dode hanyar numfashin mutum ne.

Kwayar cutar wacce bisa al'adarta take shiga ta baki, tana yin kwanaki uku zuwa hudu kafin ta tsallaka ga huhun mutum. A daidai wannan wurin mai cutar ba zai ga wata alama ba, kuma yana da damar daukar matakin fatattakarta kafin ta kama shi sosai.
Jerin abubuwan da za a kawo a qasa, matakan rigakafin cutar ne kafin ta fara illata mutum:

1. Mutum ya yawaita shan abu ruwa-ruwa kuma mai zafi sosai, kamar zallar ruwan zafi, shayi, kunu, farfesu da makamantansu, hakan yana dauraye cutar ya wurgata cikin cikin mutum inda sinadaran cikin za su halakata. A guji shan ruwan sanyi da kayan zaqi masu sanyi.

2. A kowane bayan minti 20 mutum ya guntsi ruwa mai dumi a bakinsa, ya kuskure ruwan daga bakinsa har zuwa maqogwaronsa. Ruwan ya zama mai kashe qwayoyin cuta, wato wanda ake hadawa da irin su antiseptic, ko kuma a dan sa wa ruwan dumin gishiri kadan a juya kafin a guntsa, ko a dan matse masa lemon tsami da makamantansu.

3. Kowane sabulu da omo yana kashe cutar. Idan mutum ya dawo gida daga waje, kai tsaye ya hanzarta shiga bayi ya yi wanka, sannan ya wanke kayansa, in hakan ba zai yiwu ba, ya shanya kayan a rana.

4. Cutar tana kwanciya a jikin qarafa da hannun qofa da gilashi da jikin qofa da taga da makamantan wadannan har na kwana tara cur. A daure a riqa wanke wadannan wurare a kai-a kai don kada wanda ya taba su ya dauka.

5. Banda shan taba.

6. A riqa wanke hannu a kowane bayan minti 20 da sabulu mai kumfa.

7. Mutum ya yawaita cin kayan marmari da ganyayyaki da abinci mai gina jiki (A tuntubi masana don qarin bayani).

8. Ba a daukar cutar ta hanyar dabbobi.

9. A guji duk abin da zai kai mutum ga mura, domin tana sauqaqa hanyoyin shigar cutar ga mutum.

10. Kada a yi sakaci da duk wani motsi da mutum ya ji a maqogwaronsa, kamar zafin maqogwaro ko qaiqayinsa. A hanzarta bin matakan da aka kawo a baya.

Kada a sha maganin Ibuprofen.

Ma'asumah Nigerian News Updates
Tare da Muhammad Bin Ibrahim

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post