Daga Bilal Nasir Umar Sakkwato
Yadda wata amarya ta amince da auren mijin da ake sa ran mutuwarsa ta kuma jirashi na tsawon shekaru biyu daga baya ya dawo. Amaryar mai suna Umaima Ibrahim ta amince da auren angon nata mai suna Musa Haruna ne bayan shafe shekaru biyu ba labarinsa, wanda a sanadiyar haka ya sanya tsohuwar matarsa ta nemi a raba aurensu.
Duk da ƴan'uwan mijin basu yanke ƙauna ga dawowarsa ba amma a ɓangaren tsohuwar matar tasa suka tursasa akan cewa sai an raba wannan auren, a wannan hali da yanayin da ake ciki ne dai wannan sabuwar matar tasa ta yarda ta kuma amince da ta aureshi duk da cewa akwai zarge-zargen rashin tabbas akan rayuwarsa ko dawowarsa.
Mijin ya ɓata ne tun a 12/12/2015 bayan harin da rundunar sojojin Najeriya suka kaiwa Sheikh Zakzaky a gidansa dake Zariya, harin wanda kuma ya yi sanadiyar rasa dubbanin rayukan almajiran Sheikh Zakzakin.
An sami tabbacin rayuwar wannan bawan Allah ne bayan da Kotu ta saki wasu ƙarin mutum ɗari daga cikin almajiran Sheikh Zakzaky da aka kama tun a ranar da sojoji suka ƙaddamar da harin a 12/12/2015, Kotun ta kuma wanke su daga dukkanin zarge-zargen da ake musu bayan sun shafe tsawon shekaru huɗu da ƙari a gidan kurkuku.
A ƙarshe kuma an gabatar da walimar murna da dawowarsa haɗi da walimar aurensa da amaryar tasa a ranar Laraba 4/3/2020, a garinsu dake Makina dake cikin ƙaramar hukumar mulkin Gwadabawa ta jahar Sakkwato.
Tags:
Labaran Duniya