Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya ya bayyana cewa, bai kamata a mayar da batun bullar cutar corona a kasar ya zama batun siyasa a kan kasar Iran ba.
(Rohoton abna24.com) Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a wata zantawa da ta yi da babban daraktan hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa, matsalar corona matsala ce ta lafiya wadda ta shafi duniya, saboda haka hukumarsa ba za ta amince a mayar da wannan batun ya zama na siyasa ba a kasar Iran musamman.
Ya ce yazanta da sakataren harkokin wajen kasar Aurka Mike Pompeo a kan wanna batu, inda ya jaddada masa wajabcin janye takunkuman da suke kawo am Iran matsala wajen yaki da cutar corona, ya ce a halin yanzu dai Amurka ta amince za ta janye wasu daga takunkuman.
Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya ya yi godiya ga dukkanin kasashen da suka taimaka ma Iran domin yaki da cutar corona
Tags:
Labaran Duniya