Wata Sabuwa:/ Najeriya na bukatar sabon kundun tsarin mulki - Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce Najeriya na bukatar sabon kundun tsarin mulki don ci gaban kasar nan. Ya sanar da hakan ne a taron farko na tunawa da Dr. Fredrick Fasehun, wanda ya kirkiro kungiyar jama’ar Odua (OPC) a jihar Legas. 

Tsohon shugaban kasar ya kara da cewa Najeriya dole ne ta damu da gyaran kasar nan don kawo ci gaba. Obasanjo ya jaddada cewa akwai bukatar gyara a duk fadin kasar nan. Ya ce “Najeriya na da bukatar kundun tsarin mulki sabo wanda zai kunshi burika, tsoro da kuma abubuwan da kasar Najeriya ke bukata.”

Kamar yadda ya ce, karuwar rashin tsaro a kasar nan ta assasa abubuwa da yawa da ke faruwa a kasar nan. Yace gwamnoni a matsayinsu na shugabannin tsaron jiharsu ba zasu iya yin shiru a bangaren garkuwa da mutane, daba da kuma ta’addancin Boko Haram. “Dukkan gwamnonin mu na kokarin yaki da rashin tsaro a kasar nan. Mu hada kai da hukumomin tsaro don inganta tsaron kasar nan. Idan ba mu da tsaro mai inganci, babu inda kasar mu za ta je,” yace. 

sohon shugaban kasa Obasanjo ya dau alkawarin ci gaba da tabbatar da hadin kan kasar nan har zuwa mutuwarsa. Ya jajanta rashin yarda da ke tsakanin kungiyoyi da yankunan kasar nan. Ya ce: “Yadda muke amfani da kalami wajen magana da junanmu a kasar nan tsakanin yankuna ba shi da amfani.

Zan ci gaba da kokari wajen tabbatar da hadin kan kasar nan har zuwa mutuwata. Amma wannan fafutukar ba zan yi ta don kabilata bane ko ‘ya’yana, zan yi ta ne don hadin kan mutanen kasar nan.” Tsohon shugaban kasar ya jajanta yadda ake ta magana kan raba kasar nan. 

Ya ce hakan babbar matsala ne kuma shawo kan shi zai kawo karshen wannan babbar matsalar. “Idan Boko Haram ta za ta iya samun tallafi, kowacce kungiya kuwa za ta iya samun tallafin a ciki da wajen kasar nan.” Ya ce marigayi Fasehun ya matukar nuna damuwarsa a kan yadda siyasar kasar nan ta karkace kuma zai yi matukar farin ciki idan hadin kai da gyaran kasar nan ya tabbata. FOLLOW US OUR FACEBOOK FAGE NOW
ZAINILABIDINA AHMAD SULEIMAN

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post