Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da cewa an kone motar sintirin jami`an tsaron yan sanda wacce ta kashe wata baiwar allah mai suna Hauwa Danladi-Turis yayin da tazo tsallaka titi
Motar ta raunata mutane hudu a karamar hukumar Malammadori ta jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, Abdu Jinjiri, ya sanar da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Malammadori, cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a.
Jinjiri, ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da mota take dauke da ‘yan sanda biyu tana bin wata mota da take zargi.
“yan sandan suna bin wata mota ne da ake zargi kuma yayi kokarin suna kama wannan mota hatsarin ya auku, motar ta make wata yarinya kuma ta mutu yayin da wasu mutane hudu suka raunata. “
A cikin rashin sa’a ne wasu matasa a yankin suka yi amfani da damar su wajen bankawa ababen hawan biyu wuta anan take,” ya ce.
Jinjiri ya ce ‘yan sandan da lamarin ya faru dasu a halin yanzu suna garkame kuma ana bincike a kan su.
Wani ganau ba jiyau ba, Hamza Bello, ya sanar da kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa mutane takwas ne suka samu rauni yayin hatsarin.
“Wajen karfe 8 na daren ranar Juma’a data gabata ne motar sintiri ta bi wata mota kirar Golf da gudu a kan titin Hadeja zuwa UBA.
Motar wacce ke dauke da buhunan masara da barkono ta fadi kusa da tashar mota ta Malammadori inda ta raunata mutane biyar da ke ciki tare da wasu ukun da ke kan babur a gefen titi,” ya ce.
A yayin martani a kan aukuwar lamarin, shugaban karamar hukumar, Bako Kashidila ya roki jama’ar yankin da su kwantar da hankulansu. Kashidila ya ce za a tabbatar da cewa an binciki wannan gangancin tare da yin adalci ga iyalan mamaciyar.
mudassir bara`a malumfashi
Tags:
Labaran Duniya