Wane Shiri Ka Yi Wa Talaucin Da Za A Yi A Duniya?



Cutar Corona ta janyo hasarori da faduwa a kasuwannin stocks na duniya. Haka nan zirga-zirgar jiragen sama sun ragu ainun a dalilinta. Hatta harkar otel-otel na duniya tana neman tsayawa cik dominta.

Wadannan hanyoyin samun kudi a yanzu haka sun shafi kusan kowa a duniya ta fuskoki daban-daban. Mutanen qasashen duniya da dama na zaune a gidajensu, ba sa fita saboda tsoron cutar. Abin da suka tara kawai suke ci.

Duk wadannan fa ba sa rasa nasaba da cutar hatta mu a nan Nijeria. Masu harkar Traveling Agencies yanzu komai ya tsaya mu su. Qasashe sun daina ba da visa. Kasuwar tamu stock din dama ba ta da abin fadi. Ga kuma salon mulkin Buhari wanda ya durqusar da kowace harka. Boda an garqame. Bankuna an raunana saboda tsarin TSA. Firgicin 'yan ta'adda ya tsaida qananan harkokin talakawa.

Yanzu idan da za a ba mutum miliyan 100, a ce ya je ya yi business, ba zai samu harka mai tabbas wacce zai zuba mata wannan kudi kuma ya wanye lafiya ba. Mai harkar miliyan goma ya dawo yana ta dubu dari. Mai harkar dubbai ya zama mara sisi. Su ma wadannan suna qara zafafa talaucin yanzu, suna kuma nuni da cewa talaucin gobe mai ta'azzara ne.

Dori a kan duk wadannan, NNPC ta ce 'yan Nijeriya su ja damara, domin talauci zai qara fantsama da zafafa. Saboda darajar danyen mai ta sake ruguzowa.

Shin wane shiri ka yi?

Ga shawarwari sai ka hada da naka:

1. In akwai kudi a hannunka tanadi abincin wata, ko na shekara, ko na shekaru gwargwadon dai yadda za ka iya. Abinci shi ne mataki na qarshe na kariyar talauci.

2. Rage buqatu da burace-buracen rayuwa. In ba ka da gida, zauna a na haya mai sauqi. In motoci fiye da daya gare ka, rage su. In kuma daya ce, taqaita abin da zai tilasta ka yi mata hidima. In ma babu motar, sauqaqa rayuwarka da rashinta. In kana da 'ya'ya a makarantu masu tsada, maida su makarantu masu arha. Taqaita dinkunan kece raini. Rage kalle-kallen 'yan mata da yi mu su hidima. Sa ido kan abincinka da na iyali don gudun tsokano rashin lafiya.

3. Ka damu da bin labarai don sanin halin da duniya ke ciki.

4. Kada ka yi sakaci da addu'a. Don da gaske Allah yana amsawa.


Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post