MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Daga: Abbagano ✍️
Ya kamata mu fito mu yi abinda ya dace sai Allah (t) ya saka Mana taimakonsa, domin shi Allah saika Mike ne sannan sai ya shigo da temakon sa gareka
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِن تَنصُرُوا اللَّهَ يَنصُرْكُمْ وَيُثَبِّتْ أَقْدَامَكُمْ )
محمد (7) Muhammad
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku, kuma Ya tabbatar da dugãduganku..
Yana da kyau mu tsaya mu yi abinda ya dace akan jagoranmu, sai Allah ya shigo da temakon sa.
👉Shin daka makale gida kana jiran umarnin waye don ka fito ka taimaki jagoranka?? 🤷♂
👉Ko Kuma bakaji duk sakunanan da su Sayyid suke turowa matasan Abuja ba ??🤷♂
👉Ko kamanta wayar da sukai da sayyid Muhammad bara, lokacin shahadar shahid Ahamad Rufa'i dodo??🤷♂
👉Ko maganar da su sayyid Badamasi suke fadi ba mu ji ne ba??🤷♂
👉Shin ba ka ji sakon su Sayyid da sukai wa wadanda aka saka kwananan Nan daga prison ba?? 🤷♂
👉Gaskiya ya kamata hankalin mu ya dawo jikin mu, Idan har kana tunanin sai wani yace maka sannan ka fito ka taimaki jagoran ka, lallai hakan kuskurene, tunda ai shidin koma waye' yafi jagoran nakane??🤷♂
Mu Tsaya mu dake mu tunkari azzaluman nan, Kuma na san Allah zai dafa Mana tabbas,tunda shi ya fada.
Mu tuna mu muna da Allah fa Wanda yace:
( إِن يَنصُرْكُمُ اللَّهُ فَلَا غَالِبَ لَكُمْ ۖ وَإِن يَخْذُلْكُمْ فَمَن ذَا الَّذِي يَنصُرُكُم مِّن بَعْدِهِ ۗ وَعَلَى اللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ )
آل عمران (160) Aal-Imran
Idan Allah Ya taimake ku, to, bãbu marinjayi a gare ku. Kuma idan Ya yarɓe ku, to, wãnẽ ne wanda yake taimakon ku bãyanSa? Kuma ga Allah sai mũminai su dõgara.
Mu da muke da Mai karfin da ba bu irinsa, Mai rundunar da babu irinta, Mai ikon da babu irin nasa, to shin wazai tsorata mu??
'Yan uwana kar mu ji tsoron mu tashi mu tunkare su, muyi musu fito na fito, mu fita gaba dayan mu, mu daga murya, muce
(KO MUTUWA KO ZAKZAKY)✌✌
( قَاتِلُوهُمْ يُعَذِّبْهُمُ اللَّهُ بِأَيْدِيكُمْ وَيُخْزِهِمْ وَيَنصُرْكُمْ عَلَيْهِمْ وَيَشْفِ صُدُورَ قَوْمٍ مُّؤْمِنِينَ )
التوبة (14) At-Tawba
Ku yãƙe su, Allah Ya yi musu azabã da hannãyenku, kuma Ya kunyatar da su, kuma Ya taimake ku, kuma Ya warkar da ƙirãzan mutãne mũminai.
Lallai mu kam ba mune za mu yi ba, Allah ne zai yi, bamu da karfi shine Mai karfi, bamu da wayo shine Mai wayo.
Amman shi dakan sa yace mu yi kokari sai ya nunana Mana hanya.
وَالَّذِينَ جَاهَدُوا فِينَا لَنَهْدِيَنَّهُمْ سُبُلَنَا ۚ وَإِنَّ اللَّهَ لَمَعَ الْمُحْسِنِينَ )
العنكبوت (69) Al-Ankaboot
Kuma wadannan da suka yi ƙõƙari ga nẽman yardarMu, lalle Munã shiryar da su ga hanyõyinMu, kuma lalle Allah, tabbas, Yanã tãre da mãsu kyautatãwa (ga addĩninsu).
Tags:
#FREE_ZAKZAKY