UPDATE; Mahaifana Suna Cikin Tsananin Rashin Lafiya.



Yau dai zan yi Magana akan dokar da ba rubutacciya ba, amma kuma ake aiwatar da ita wajen cutar da mahaifana; a tsammanina shurun da na yi zai taimaka wajen rage irin ukubar da mahaifana suke fuskanta.

Tun mahaifana na tsare a wajen DSS, kafin a mayar da su gidan kurkukun jihar Kaduna; mahaifina na fama da hawan jinni sosai, watarana jininshi ya hau, watarana ya sauka; kullum dai haka yake fama da jiki, banda sauran nau’ikan rashin lafiya da yake fama da.

Mahaifiyata kuwa, bayan dukkan matsaloli na rashin lafiya da take fama da shi, a yanzu haka jini ne yake zuba ta bakinta da hanci; saboda dama ta na fama da wani ciwo mai suna Sinus, wanda ko kadan a taba yi mata magani ba a cikin shekaru biyar din da suka wuce.

A karshen watan Disamba an ba wasu likitoci damar ganinsu, wadannan likitocin sun bukaci a wasu gwaje-gwaje; daga cikin gwaje-gwajen akwai wadanda dole sai an fita da su zuwa asibiti, amma shugabannin gidan yarin suka hana; a cewarsu sai kotu ta amince da hakan.

A ranar 24 ga watan Fabrairu, kotu ta basu umarnin da su bari ayi musu duk abinda ya dace na magani, a ranar 26 likitocin sun sake bukatar ayi wadannan gwaje-gwajen kamar yadda suka bukata a baya; inda muka yi iya kokarinmu don ganin hakan ya faru.

Bayan makonni na shirye-shirye, alkawura don ganin likita da ma asibiti; da ma wasu shirye-shirye da muka yi da shugaban gidan yari na jihar Kaduna, hakarmu ta kasa cimma ruwa, saboda shugabannin gidan yarin sun sake mana cikas kamar yadda suka yi a baya.

Daya daga cikin likitocin mahaifana, wanda shine zai yi gwaje-gwajen; dama kuma shi kadai ne aka bari ya dinga duba mahaifana, ya shaida mana cewa shugabannin gidan yarin sun bukaci da shi da sauran likitocin su rubuta bukata a rubuce, wacce a cewarsu za a kai Abuja domin neman amincewa daga sama.

Don haka a cewarsu dole ne mu zauna da babban likitan gidan yarin jihar Kaduna, da kuma likitan da yake wakiltar jihar Kaduna; a duk sanda suke da lokacin mu zauna da su din. Daga nan sai mu sake bin matakan da muka dauka a tsawon makonni uku, don sake sanya lokacin da za a gudanar da gwaje-gwajen a lokacin da ya musu.

Sannan sun shaidawa likitan cewa ba a yarda a gudanar da wadannan shirye-shiryen tare da wani lauya ba. Muazu Dan Musa wanda shine shugaban gidan yarin jihar Kaduna, ya bayyana cewa muddin aka yi kokarin sanya lauya a dukkan shirye-shiryen; to kamar anyi aikin banza ne, don kuwa a cewarshi in aka yi hakan komai ya rushe kenan. Wato ma’ana ba zasu sake bari likitoci su duba mahaifana ba.


Mohammed Ibraheem Zakzaky

13/03/2020.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates. 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post