MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Daga: Bin Haroun Sigau
Na saka wa wannan rubutu nawa wannan taken ne, domin ankarar da yan uwa kan abinda ake shirin yi, don banga abin farin ciki ba anan. Na'am ta wani bangaren zamu iya yin farin ciki, ko ba komi makiyin mu, Allah ya nuna masa karfin iko, ya kwace ikon da dashi ne yake samun damar yin abinda yake yi akanmu da fadar maganganu batanci akan yan uwa.
Ta daya bangaren kuma in muka kalli lamarin wanene ya sauke shin sai muga kamar yanzu dariya ba namu bane, domin shine azzalumin daya assasa dukkan makiricin da har aka karkashe mana yan uwa, bayan Wakiar Zaria harma da abinda ya faru da yan uwa a tattakin yankin Kano.
In muka saka abubuwan a cikin tunani da yin nazari mai kyau, zamu ga cewa; wanda ya aikata hakan ne gare mu zai kawo wani wanda zai ràngwanta wa yan uwan mu? Sam wannan bashi ne abin hange ba, me zai biyo baya na wannan cenjin da sukayi? Nijeriya wata kasa ce mai cike da azzalumai iri-iri, baka taba ganin an sauke wani an dora wani, wanin da aka dora ya fi wanda aka sauke tausayi da kokarin kawo gyara.
Bakin su daya, halayyar su daya, basu bawa kowa mulki sai wanda ya yarda zai bi umurnin su na zalunci, da cika muradan su. Tabbas, Sunusi a dokar siyasar su yayi laifi, amma ba wannan ne yasa suka tunbuke shi karfi da yaji ba, akwai abinda zuke so su cimma ne wanda basu samu daga gareshi ba. Ko kuma suke ganin nan gaba zai hana su cimma wa in har yana kan karagar mulki.
Azzalumi dai ko ina yake sunansa azzalumi, mu kuma mun barranta dasu, dà ayyukan su, bama tare dashi ta ko wanne janibi, ya cutar damu ne ko kumà yan uwan mu, yan uwan nan namu a ba addini ne ko kumà yan uwan mu na jinsi, kowa yana da yanci da kuna hakki àkan mu, muga yana samun rayuwa mai kyau. Don haka yan uwa na Kano ku shirya fiskantar sabon azzalumin sarkin ku, domin tsakanin mu da azzalumai bara'a ce da neman tsari daga Allah.
Baku tare da Sunusi bàlle Aminu Ado, domin uwarsa daya ubansu daya, kowa aiki yake don biyan bukatun uwayen gidan sa... Duk da dai Nadan yi farib ciki, da aka ce yayi maganar cewa; an dora komi ne bisa Sunnah, kana kuma saida aka bi duk wata hanya data dace aka sauke shi akan Sunnah. Allah ya kare mu sharrin masharran ta, da azzalaumai.
Tags:
Daga marubata