Tsoro bala'i ne, Jama'a banda tsoro!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

TSORO YA SA SHI LASHE AMAN DA YAYI

Tabbas, tsoro bala'i ne kamar yadda wannan babban malamin Izala ya fada, domin tsoro kan sa mutum yayi riddah .

Wani lokaci kuma yakan sa mutum ya qaryata gaskiya ko kuma ya gaskata qarya. Idan kuwa haka tsoro yake, to, ya zama bala'i, sai dai muyi addu'ar Allah ya ranba mu da shi (tsoron).

Tunda kuwa hakane, to, lalle wanda tsoro zai sa shi ya qaryata gaskiya ko gaskata qarya bai cancanta ya zama shugaba ko jagora ba, ko da kuwa shugabancin wasan yara ne ballantana na addini.

Cikin farkon lokacin da Saudiyyah ta bayyana hana yin sallah cikin jam'i ne wannan malami ya qalubalanci dokar da kakkausar murya, kuma ya nuna rashin goyon bayansu da wannan doka.

Wannan magana ta shehin malamin ta tasirantu cikin 'ya'yan qungiyarsa, yadda takai suna qalubalantar wannan doka anan cikin gida Nigeria.

KARANTA WANNAN:-Coronavirus ko dai Makircin Yahudu 3


Tabbas, ra'ayin wannan malami a wancan lokaci daidai ne, domin ita ce tayi daidai da shari'ah. Bai kamata a goyi bayan Yahudu kan ra'ayinsu na cutar da muslimci ba.

Sai dai wani abin takaici, bayan gwamnati ta gana da wannan shehin malami don ya amsa wasu 'yan tambayoyi, sai ga shi ya fito yana lashe aman da yayi a tsaye ko risnawa.

Duk wani abinda ya fito ta baki bayan ya zauna a ciki, to, sunan wannan abu Najasa, bai halatta ga musulmi ya qara cinsa ba komai yunwa !

ABINDA BA A TABA SAMU BA KENAN, KUMA BA ZA A SAMU BA TARE DA SAYYID ZAKZAKY (H), YIN MAGANA SANNAN AZO DAGA BAYA A CANZA.

Yaa Allah ka barmu tare da Sayyid Zakzaky (H), ka ba shi kariya tare da dawo mana da shi cikinmu.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

08126385034-09039791509

~30th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post