@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ILIMI BA ABINDA YA BARI
Wannan shine abinda ke rikitar da qwaqwalen masu qaramae qwaqwalwa da tsukekken tunani, wanda hakan yayi sanadin suna kafirta 'yan'uwansu musulmi masu kawo hotunan magabata.
A fahinta ta mazhabin iyalan gidan Ma'aiki (S.A.W.W)ana iya samar da hotunan A'imma (A.S)wanda da zarar ka gani za ka iya cewa ai wannan Imam wane ne, alhali a zamaninsu ba a daukar hoto ballantana ace daukarsu aka yi.
To, su 'yan'uwanmu Ahlus-Sunnah sun jahilci wannan abu wanda ya kutsa su cikin kafirta mu da kuma alaqantamu da kiristoci masu kawo hoton Isah Almasihu (A.S).
Hanyar samar da hoton wanda ya gabata shine, samun ilimi na sanin haqiqanin siffar mutum ta zahiri, sai kuma ilimin zane (Arts).
Duk wanda ya qware da zane, kuma ya sami mai ilimin siffanta mutum ya siffanta masa shi, to, zai iya samar da hotonsa wanda duk wanda ya san shi zai iya cewa ai wannan wane ne. Yadda ake zana mutane a wannan zamani kadai ya isa zama abin misali ga masu ilimi da hankali.
Ku biyo ni cikin wannan hadisi da Bukhari ya riwaito shi lamar haka;
‘’ Yahya Bn Sulaiman ya bamu labari yace, Ibn Wahab ya bani labari yace, Amruu ya bani labari cewa;lalle Bukhaira ya ba shi labari daga Kuraibin Bawan Ibn Abbas, daga Ibn Abbas (R.A)yace, Annabi (S.A.W.W)ya shiga wani gida sai yaga hoton Ibrahim (A.S)a cikinsa da hoton Maryama (A.S), sai yace;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ KU KAWAR DA SHI, HAQIQA NA JI (cewa)MALA'IKU BA SA SHIGA GIDAN DA YAKE DA HOTO. AI WANNAN IBRAHIM NE AKA SURANTA SHI....‘’
(Bukhari, hadisi me lamba 3351).
A hadisi na 3352 kuma aka ce hoton Isma'il da Ibrahim (A.S)ne ya gani.
TAMBAYA
――――――
Shin, a zamanin Annabi Ibrahim da Isma'il (A.S)ana daukar hoto ne?
Idan amsa ita ce, ba a dauka. To, ta yaya aka samar da hotunansu har Annabi ya gani yace sune?
‘’ FA'ATABIRUU YAA ULUL ALBAAB !‘’
Yanzu hoton wa kuke gani anan?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034-07059911360
~3rd March, 2020.
Tags:
Taskar ilimi