Tambaya: Shin, jami'an tsaro na tsare kamuwa daga Coronavirus ne??



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

TAMBAYA GA GWAMNATIN NIGERIA

Cikin matakan kariya da gwamnati ta dauka don kare al'ummar qasarta don rage kamuwa daga cutar covid-19 ta rufe makarantu tare da bada hutu ga qananan ma'aika dake mataki na 12 zuwa qasa.

Wannan mataki da ta dauka zai rage cunkoson jama'a a ma'aitu na kowanne sassa.

Abu guda da suka rage shine, rashin bawa jami'an tsaro wannan hutu alhali suna da qananan ma'aita cikinsu wadanda ba su wuce mataki na bakwai (GL 07)ba.

             TANBAYA
           __________

(1)- Shin, su jami'an tsaron ba kwa tausayawa rayuwarsu ne ko kuma suna bada kariya ne wajen hana kamuwa daga cutar coronavirus?

(2)- Idan amsa ita ce a'a, suna bada kariya (tsaro)ne ga al'umma. To, tambaya anan ita ce,

Tsakanin jami'an tsaro da cutar coronavirus waccece tafi saurin kamu da kisan al'umma?

(3)- Tsakanin jami'an tsaro da covid-19 wannene yafi saurin cutar da al'umma?

(4)- Shin, ko su ba sa kamuwa daga wannan cutar ne?

(5)- Idan kuma suna kamuwa, to, me yasa ba za ku bawa qananan su hutu don rage cunkosonsu ba?

Ni dai a tawa fahintar jami'an tsaro sun fi kashe al'ummar qasa fiye da yadda cutar coronavirus ke kashe al'umma.

Hujjata kan haka ita ce, cikin wata guda (1)da ake fama da barazanar cutar covid-19 har zuwa yau ba a sami mutane 100 da ke dauke da wannan cuta a wannan qasa tamu Nigeria ba, kuma ba a sami mutane 10 da ta kashe ba.

KARANTA NAÑ:
Duk mai nisan kwana zaiga ƙarshen wannan zaluncin da idon sa

Neman kashe Sayyid Zakzaky da sunan Coronavirus a gidan yarin Kaduna

Su kuwa jami'an tsaro sun kashe talakawa sama da mutum 1,000 cikin kwana biyu (2), kuma sun jikkata sama da mutum dari (100).

Sannan kuma coronavirus ba ta cutar da jama'a kamar yadda jami'an tsaro ke cutar da su.

Za ka iya samun mutum dubu (1,000)na mu'amalar kasuwanci ko aiki amma ba za sami mutum 30 da ke tsoron wata aba wai covid-19 ba. Amma da za ka sami jami'an tsaro na kai-kawo (zirga-zirga)cikin gurin da al'umma 1,000 ke mu'amala, to, wallahi ba za raka mutane 100 da ke cikin fargabar cutuwa daga gare su ba.

Ba wai batun mai ha'inci ko mai laifi ba, a'a, mai gaskiyar ma ba shi cikin aminci game da su, domin za su iya cutar da su ko da ba bisa laifinsu ba.

(6)- Wa ya fi cancanta a dau matakin hana shi cutar da al'umma tsakanin covid-19 da jami'an tsaro?

Wannan dai fahintata ce, amma dai muna buqatar amsar wadannan tambayoyi daga gare ku gwamnatin Nigeria.

~31st March, 2020.

                F
                R
                E
                E

SAYYID ZAKZAKY (H)!

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post