Soyayya: Bayani game da so, haɗi da sharuɗɗan sa!!




🇳🇬 Ma'asumah Hausa Nigerian News Updates


    Da Farko dai yana da kyau mu San Ma'anar SO kafin mu San sharudan da suke rataye a wuyan duk Wanda ke bin Mazhabar sa.
Masana da yawa Na ta fashin baqi akan ma'anonin so, kowa kuma akwai irin Yadda yake fassara shi ta fuskar da ya fahimce shi..

A sahihiyar Magana So yafi Kama da a Kira shi:-
#SO Wani Qawa-zuci ne mai qarfi dake dauke da abubuwa 4
√ Kulawa
√ Kishi
√ Sha'awa
√ Buri da Muradai

Rashin daya daga cikin wayannan kan jawo gurguncewar So kai-tsaye.

SHARUDAN SOYAYYA

Maudu'in Maganar tamu kenan; So na da sharuda wadanda akan su ne so ya ke dorewa, bayan ginuwarsa a zukatan masoyan juna..
Sune kamar haka:-

(1) *Sauke Jin-kai da Izza;-* Musamman ga Mace, saboda tana da kyau ko mulkin mahaifinta ko sarautarsa, ko fifikon shekarun namiji akan mace yana nuna Mata shi babba ne kullum.

(2) *Yafiya da Uziri*:- Haqiqa duk soyayyar da aka rasa wannan sharadin dab take ta Rushewa domin masoyi ba Mala'ika bane da za'a ce bazai yi laifi ko kuskure ba.

(3) *Raha da wasa da zolaya*;-  Zaku yarda dani idan na fada muke cewa kowacce Mace tana son nishadi da raha, matsawar Namiji ba mai irin barkwancin nan bane shi wai koda yaushe Wa'azi, fada, zantuka irin Wanda Yayunta suke mata to haqiqa za,a rasa 70% Na soyayyar juna.

(4) *Cika Alqawari da kyautatawa duk qanqantarta*  Shi dai cika alqawari ai wajibi ne ba sai a soyayya ba.. Sannan kyautatawa ance sadakin soyayya.. Daga nan ma nasan kun je Gano.

(5) *Girmama Juna*:- Ba wai kuna durqusawa juna ba idan zaku gaisa ake nufi ba. A'a kulawa da maganganu masu ma'ana yayin fira, ta yadda bazaku Na amfani da lafuza masu harshen damo ba Misali.. " Ki Gaisar min da Babar ki" kunga yana daukar ma,anar zaagi. A'a ace " Ki Gaisar min da Mama" Zai fi.

Daga qarshe.. Masoyi Rahama ne domin gareshi zuciya ke fakewa, sabida a tare dashi take samun Nutsuwa da Farinciki da Walwala..
 Kada mu kasance masu qoqarin muzantawa masoyanmu.. Mu Alkinta musu abin da suke so  domin bamu da sama da su a rayuwa.

 @Muh'd Aliyu Daud (Dansudan) Azare.

 Ku ziyarce a shafinmu don samun labarai da muqaloli masu amfanarwa! Labarai cikin gida daj na waje,  ta wannan  link:- Ma'asumah Nigerian News Update 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post